Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ana zargin ɓarkewar cutar Sanƙarau (Cerebrospinal meningitis) ta yi sanadin mutuwar wasu dama kuma mafi yawa yara a ƙauyen Kurawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato wanda ya haifar da damuwa a tsakanin al’umma a yayin da jami’an lafiya ke kokawar ganin sun kwantar da cutar.
Mazauna garin sun ce makonni uku kenan da suka wuce da ɓarkewar cutar a yayin da aka fi samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar a ‘yan kwanakin bayan nan.
Mudassir Kurawa, dagacin garin, ya shaida wa manema labarai cewa an samu mutane tsakanin 10 ko 15 da suka rasu a garin idan aka cire wasu da suke zaune a kewayen garin.
“Yawancin waɗanda abin ya shafa ya yara ne da ke tsakanin shekaru 2 zuwa 10,” ya fada.
Ya ƙara da cewa a ranar Asabar kaɗai, an kwantar da marasa lafiya 15 a asibitin garin a yayin da uku daga ciki suka riga mu gidan gaskiya jim kaɗan bayan kwantar da su.
Wani jami’in lafiya a garin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana da jama’a, ya ce, yawan mutanen sun fi ƙarfin asibitin.
“Mutane na ta taruruwa zuwa asibitin a kullum domin neman magani. Yawansu ya sha kanmu,” inji majiyar.
Mazauna garin sun ce alamomin da suka riƙa gani ya haɗa da ciwon wuya da zazzaɓi mai zafi da amai da gudawa da fita daga hayyaci waɗanda duk alamomi ne da suke nuna kamuwa da Sanƙarau.
ɓarkewar cutar ta jawo damuwa game da batun sa ido kan ɓullar cutattuka da ɗaukin agajin gaggawa da damar samun kulawar lafiya a Nijeriya a wuraren da ake fargabar kamuwa da Sanƙarau.
Wasu mazauna sun ce waɗnda suka kamu da cutar suna mutuwa ne cikin awanni 24 da zarar sun fara jin alamomin kamuwa da cutar wanda hakan ya jawo fargaba game da batun jinkiri da taƙaitar damar magance sutar.
“An faɗa mana cewa Sanƙarau ce, amma kuma ana ta samun masu mutuwa,” in ji wani mazaunin garin.
Kwamishinan lafiya a jihar Sakkwato, Faruk Wurno ya ce, gwamnatin jihar ta tura jami’an lafiya domin su gidanar da bincike da ba da magani kyauta.
“Na samu rahoton ne a ranar Lahadi kuma nan da nan na tura jami’an lafiya domin su duba lamarin da tallafa wa al’ummar da abin ya shafa,” ya faɗa.
Wurno ya ƙara da cewa mahukunta na aiki domin gano adadin mutanen da lamarin ya shafa bayan ɓarkewar cutar.
Cutar Sanƙarau yawanci bakteriya ce ke haifar da ita wanda ke haifar da kumburi a wani sashe na ƙwaƙwalwa da yanki na ƙashin baya. Alamomin kamuwa da Sanƙarau sun haɗa da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai da sanƙamewar wuya. Sai dai akwai allurar rigakafin kamuwa da bakteriyar da ke haifar da cutar.
Yankin Arewacin Nijeriya na cikin yankunan da Afirka ake da fargabar kamuwar da Sanƙarau saboda zafin da ƙura da yanayin cunkoson wurin zaman al’umma wanda ke haifar da ɓarkewar cutar.
ƙwararru a fannin lafiya sun sha gargaɗin cewa akwai buƙatar mihimmanta allurar rigakafin da ƙoƙarin gano cutar da wuri wajen rage yawan masu rasa rayuka sakamakon cutar.
Wannan lamari na baya-bayan nan ya fito da irin fargabar da ake da ita a fannin lafiya a karkara da yanayin da ke sauya wajen haifar da barkewar cuta wanda kan haifar da buƙatar agajin gaggawa.
