Kotu ta dakatar da sayar da kadarorin Shoprite kan bashin biliyan N1.76

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas ta hana shugabannin kamfanin Shoprite sayar da duk wani kadara ko hannun jari na kamfanin har sai an biya bashin hukunci da ya kai Naira biliyan 1.76 gaba ɗaya.

Alƙalin kotun, Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa, ne ya bayar da wannan umarni bayan wata buƙata ta gaggawa da aka shigar a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, domin tabbatar da aiwatar da hukuncin sulhu da kotu ta riga ta amince da shi tun ranar 22 ga Yuli, 2025.

Baya ga hana sayar da kadarori, kotun ta kuma umurci shugabannin kamfanin Shoprite da su bayyana dukkan kadarorin kamfanin — na motsi da waɗanda ba sa motsi — ga wanda kotu ta yanke wa hukuncin biyan bashin.

Lauyan mai bin bashin, Tobenna Nnamani, ya nemi kotu ta bayar da umarnin rufe asusun kuɗaɗen kamfanin a bankuna daban-daban ta hanyar tsarin “garnishee order nisi”, domin tabbatar da karɓar kuɗin da ake bi.

Bayan samun wannan umarni, lauyoyin masu bin bashin sun buƙaci cikakken bayani daga ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin, Jide Ogundare, da sauran shugabanni, ciki har da bayanai kan cibiyar rarraba kaya da ke Ajao a Legas da kuma duk wasu haƙƙoƙin kasuwanci na kamfanin.

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga Mayu, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarin matakai.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na kotu ya samo asali ne daga gazawar kamfanin Shoprite wajen bin yarjejeniyar sulhu da kotu ta amince da ita, lamarin da ya kai ga ɗaukar wannan tsauraran mataki na dakatar da kadarorinsa.

Matakin na kotu na nuni da ƙoƙarin tabbatar da cewa kamfanoni suna mutunta hukuncin kotu da kuma cika alƙawurran da suka ɗauka a gaban doka.

By ukarofi