Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da ƙarar da kamfanin sadarwa na 9Mobile (wanda ke aiki a ƙarƙashin sunan Emerging Markets Telecommunications Services Ltd) ya shigar, inda ta tabbatar da hukuncin biyan dala miliyan 43.3 da aka yanke masa a shari’ar sasanci, tare da zora masa tarar Naira miliyan 20 kan abin da ta kira “ƙarar da ba ta da tushe”.
Hukuncin ya fito ne daga kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Tyjani Abubakar, wanda ya tabbatar da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da kuma Babbar Kotun Tarayya da suka bai wa kamfanonin AFDIN Ventures Ltd da DIRBIA Nigeria Ltd nasara.
Kotun ta bayyana cewa ƙarar da 9Mobile ya shigar ba ta da wata hujja mai ƙarfi, don haka ta dace a yi watsi da ita gaba ɗaya.
Asalin rikicin ya samo asali ne daga wata ƙara da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tun 2018, inda kamfanonin AFDIN da DIRBIA suka nemi a biya su kuɗaden da suka kai dala miliyan 13.3 da kuma dala miliyan 30.03.
Daga bisani, an miƙa shari’ar zuwa sasanci bisa yarjejeniyar ɓangarorin, inda mai sasanci guda ɗaya ya yanke hukunci na ƙarshe a shekarar 2022, wanda ya umarci 9Mobile da wasu da su mayar da kuɗaɗen ga masu ƙara.
Sai dai kamfanin ya ƙalubalanci hukuncin a kotu, yana mai cewa babu hurumin gudanar da sasancin. Amma Kotun ƙoli ta yi watsi da wannan hujja, tana mai jaddada cewa ba za a iya gujewa alhaki ba bayan an amfana da yarjejeniya.
Mai shari’a Abubakar ya ce Kotun ƙoli ba za ta amince da ƙarar da ke kawo cikas ga martabar ƙasar a idon ƙasashen duniya ba, yana mai gargaɗin cewa dole ne a kiyaye dokoki da umarnin kotu.
Kotun ta kuma soki 9Mobile kan rashin bin umarnin kotu na ajiye kuɗin da aka yanke masa a baya, tana mai cewa duk wanda ya raina umarnin kotu ba ya da damar neman jin ƙara a gabanta.
Haka kuma, kotun ta yi watsi da hujjar kamfanin cewa bai sanya hannu kai tsaye a yarjejeniyar sasanci ba, tana mai cewa duk wanda ya amfana da yarjejeniya ba zai iya kauce wa alhaki ba.
Kotun ta ƙara da cewa manufar sasanci ita ce kauce wa tsawaita shari’a a kotu, kuma duk wanda ya amince da ita dole ne ya mutunta sakamakon da aka samu.
A ƙarshe, kotun ta tabbatar da hukuncin biyan dala miliyan 43.3 tare da ƙarin Naira miliyan 20 a matsayin tarar kotu, lamarin da ya zama babban darasi ga kamfanoni kan muhimmancin bin doka da mutunta yarjejeniyoyi.
