Cece-kuce ya ɓarke bayan wata ta zargi MTN da hannu a cire kuɗi daga asusun bankin mahaifiyarta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ’yar Nijeriya ta janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta bayan ta zargi kamfanin sadarwa na MTN da hannu a wani zargin cire kuɗi ba tare da izini ba daga asusun bankin mahaifiyarta.

Matar, wadda aka bayyana da sunan @ButterBibi a dandalin ɗ (tsohon Twitter), ta yi iƙirarin cewa an cire sama da Naira 70,000 daga asusun mahaifiyarta a yanayi da ba a bayyana ba.

A cewarta, bayan faruwar lamarin, mahaifiyarta ta je banki domin kai ƙorafi, inda aka sanar da ita cewa tsohuwar lambar wayarta ta MTN an sake ba wa wani mutum, wanda ake zargin yana da alaƙa da ma’amalar da ta janyo cire kuɗin.

Lamarin ya haifar da tambayoyi masu yawa, musamman dangane da tsaron bayanan sirri da kuma yiwuwar samun damar shiga bayanan mutum ta hanyar tsohuwar lambar waya da aka sake sayar wa wani.

Ta rubuta a shafinta cewa: “An cire fiye da N70,000 daga asusun mahaifiyata. Da ta je banki, sai aka ce tsohuwar layinta ta MTN an ba wani, kuma shi ne ke amfani da shi wajen cire kuɗin. Wannan ya ba ni mamaki—shin ana iya samun damar bayanan mutum haka kawai?”

Martanin jama’a ya yi yawa a shafukan sada zumunta, inda wasu suka bayyana irin makamancin abin da ya same su, yayin da wasu suka ba da shawarwari kan yadda za a kare kai, kamar sauya lambar waya a banki da kuma sabunta bayanan BVN idan an rasa layi.

Masu sharhi sun kuma jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin kariya kamar imel da manhajojin banki maimakon dogaro da lambobin waya kawai wajen karɓar sanarwar ma’amala.

Duk da haka, har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga MTN ko bankunan da abin ya shafa domin tabbatar da ko ƙaryata zargin.

Lamarin ya sake jawo hankali kan matsalar tsaron bayanan sirri da kuma haɗarin da ke tattare da sake rarraba lambobin waya, musamman idan suna da alaƙa da muhimman asusun kuɗi.

By ukarofi