Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dubban ’yan Nijeriya masu amfani da layukan sadarwa na iya samun sauƙi nan ba da jimawa ba, bayan da Kotun Tarayya ta yanke hukunci guda biyu da suka rusa hujjar doka da ta sa aka dakatar da ba da rancen kati da data a watan Afrilu.
Waɗannan ayyukan rance, ciki har da ɗtraTime na MTN da kuma shirye-shiryen aron data na Airtel, an dakatar da su ne sakamakon sabbin ƙa’idojin lamunin dijital da Hukumar Kula Gasa daKare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta Nijeriya (FCCPC) ta kafa.
Dakatarwar ta jefa miliyoyin masu amfani da layuka cikin mawuyacin hali, musamman masu ƙaramin ƙarfi da ’yan kasuwa, waɗanda ke dogaro da wannan hanya wajen samun katin waya cikin gaggawa.
A wani muhimmin mataki, Kotun Tarayya da ke zama a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. Lewis-Allagoa, ta bayar da umarnin wucin gadi a ranar 15 ga Afrilu, inda ta hana FCCPC aiwatar da wasu muhimman tanade-tanaden dokar lamunin dijital ta 2025 a kan mambobin WASPAN.
Kotun ta kuma hana hukumar ɗaukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga ayyukan kamfanonin sadarwa a cikin tsarin da ake bi a halin yanzu.
Bayan kwanaki kaɗan, wata Kotun Tarayya a Abuja ta sake fitar da wani hukunci mai ƙarfi a wata ƙara da ta shafi kamfanonin Nairtime Holdings Limited da Nairtime Nigeria Limited. Kotun ta hana MTN da Airtel taƙaita damar kamfanonin yin amfani da muhimman hanyoyin sadarwa kamar USSD, SMS da sauran tsarin cajin kuɗi bisa dalilin sabbin ƙa’idojin FCCPC.
Haka kuma kotun ta jaddada cewa ba za a iya karya sharuɗɗan yarjejeniya ko wuce ƙa’idojin warware saɓani ba a ƙoƙarin bin sabbin dokoki.
Waɗannan hukunci biyu sun raunana dalilan da kamfanonin sadarwa suka bayar na dakatar da aikin, lamarin da ya ƙara haifar da fatan cewa za a maido da su nan ba da jimawa ba.
Rigimar ta samo asali ne daga saɓanin iko tsakanin hukumomi. FCCPC ta faɗaɗa ikon ta a 2025 zuwa harkar lamunin dijital, amma masana’antar sadarwa na ganin cewa Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ce ke da cikakken iko a kan irin waɗannan ayyuka.
A sakamakon wannan rikici, kamfanonin sadarwa suka dakatar da sabis ɗin domin kaucewa hukunci, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a.
Yanzu dai hankula sun karkata ga yadda MTN da Airtel za su gaggauta dawo da sabis ɗin da miliyoyin ’yan Nijeriya suka rasa na tsawon makonni.
