PRP ta shirya shiga zaɓe na 2027 a Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jam’iyar PRP a jihar Katsina ta ce ta shiga zaɓe daga matakin kansila har zuwa kujerar Gwamna a jihar Katsina.

Shugaban jam’iyar reshen jihar Alhaji Hassan Hamisu Ƙanƙara ya sanar da haka da yake gabatar da jawabi a wajan taron shugabannin jam’iyar na ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Katsina.

Ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyun adawa ba zai hana jam’iyar su ta PRP taɓuka komai ba .

Hamisu Ƙanƙara ya ƙara da cewa tuni jamiyar ta tantance tare da fidda yan takara na kowane muƙami a jihar.

“Duk da cewa jam’iyar mu ta talakawa ne, al’ummar jihar na tare da mu saboda kowa yaji a jikin sa”inji Ƙanƙara.

“Kada gwamnatin APC shi yafi Kowane abu sauƙi duba da halin ƙunci da suka jefa yan Najeriya na rashin tsaro,ba wuta ga tsananin takaice,”ya ce.

Hassan Ƙanƙara ya yi kira ga ya’yan jamiyar da su tashi tsaye wajan shiga ƙauyuka da birane domin tallata manufofin jam’iyar a faɗin jihar.

“Kamar yadda ka gani shugabanni da sakatarori na jam’iyar daga ƙananan hukumomi 34 da ke jihar suka halarci taron ba tare da wani ya basu ko sisi ba wanda hakan yanu al’ummar jihar Katsina PRP suka sa a gaba,”inji shugaban jam’iyar

By ukarofi