Kotu ta umarci SERAP ta biya diyyar miliyan N100 ga jami’an DSS kan ɓatanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta umarci ƙungiyar kula da tabbatar da gaskiya da adalci ga ‘yancin al’umma (SERAP) ta biya jami’an DSS biyu diyyar Naira miliyan 100 bisa zargin ta da ɓata suna.

Haka kuma, kotun ta umarci SERAP da ta biya Naira miliyan 1 a matsayin kuɗin shari’a, tare da wallafa neman afuwa ga jami’an a shafinta na X da kuma a jaridu da gidajen talabijin na ƙasa.

Hukuncin ya biyo bayan wata sanarwa ne da SERAP ta fitar a shekarar 2024, inda ta zargi jami’an DSS da kai samame ba bisa ƙa’ida ba a ofishinta da ke Abuja.

Saidai daga baya DSS ta ce binciken da ta gudanar ya wanke jami’an daga zargin, lamarin da ya sa suka kai ƙara a kotu suna neman diyyar Naira biliyan 5.5.

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Halilu Yusuf ya ce kalaman da SERAP ta wallafa sun ɓata martabar jami’an a aikinsu, don haka ta zama dole ta biya diyyar.

Kotun ta kuma umarci a riƙa ƙara kashi 10 cikin 100 na ruwa a kan kuɗin daga ranar yanke hukunci har zuwa lokacin da za a biya gaba ɗaya.

By Babaji