Wajibi ne yankunan Abuja da Kaduna su ba jiragen ƙasa da kayayyakinsu kariya – NRC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta yi kira ga yankunan da ke kusa da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da su ba jirage da kayayyakinsu kariya daga hare-hare da lalata su da ke cigaba da faruwa a kisa da su.

Wannan na zuwa ne a daidai da ayyukan ɓata-gari da lalata kayayyakin suka yawaita, lamarin da NRC ta yi alla-wadai da shi da babbar murya musamman ganin yadda ɓata-garin suke cin karensu babu babbaka a layin dogon.

A cewar NRC, al’amarin na kwanan nan ya faru ne daga kilomita 177 na Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka taru suka riƙa jifar wani jirgi da ya yi jigilar fasinjoji, lamarin da ya yi sanadin damejin wani sashe na gilashinsa.

Haka kuma, hukumar ta ce acikin mako biyu da suka gabata, an samu aukuwar makamancin haka a wasu yankuna ciki har da Gidan Busa da ke ƙauyen Sarkin Gora da ke Gundumar Kakau na Ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna da sauransu, waɗanda ke nuna matakin haɗari da jirage, mutane da ayyukan hukumar ke fuskanta.

Hukumar gudanarwar NRC ta bayyana cewa ire-iren al’amarin sun faru a wurare guda shida da ke yankin layin, wanda ya ƙara ta’azzara ƙalubalen da halin ayyukan ke fuskanta da ke shafar sufurin ‘yan Nijeriya bisa inganci.

By Babaji