WPFD: Wajibi ne kafafen labarai da gwamnatoci su haɗa kai don magance labarai masu ruɗarwa – Idris

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen yaɗa labarai, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki su ƙara haɗa kai domin magance yaduwar labaran karya da na bata-gari, tana mai jaddada cewa hakan na da matukar muhimmanci wajen kare amincewar jama’a da kuma zaman lafiyar kasa.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin Ranar Ƴan Jarida ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Radio House.

Ya ce, gwamnati na da ƙudiri wajen kare ‘yancin ‘yan jarida kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da samar da yanayi mai kyau da tsaro domin gudanar da aikinsu cikin ‘yanci da gaskiya.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na daukar matakai don inganta gaskiya da samun bayanai ga jama’a, ciki har da aiwatar da dokar ‘Freedom of Information’ da kuma karfafa hulda da kafafen yada labarai.

Haka zalika, ya yi nuni da hadin gwiwar Najeriya da UNESCO wajen kafa cibiyar Ilimin Kafafen Labarai da Bayani (IMILI) a Abuja a matsayin wani mataki na bunkasa fahimtar jama’a kan yadda ake tantance bayanai a zamani na dijital.

A nata ɓangaren, Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Binyerem Ukaire, ta jaddada bukatar karin hadin kai domin tinkarar kalubalen da ke tattare da yaduwar labaran karya, musamman a kafafen zamani.

Gwamnatin Tarayya ta sake nanata aniyarta ta aiki tare da kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula da na kasa da kasa domin gina ingantaccen tsarin yada bayanai da zai karfafa dimokuradiyya da hadin kan kasa.

By Babaji