Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE
Masu ruwa da tsaki a fannin horas da malamai a Najeriya sun yi kira mai ƙarfi kan buƙatar sake fasalin tsarin kwalejojin Ilimi domin su zama cibiyoyin koyon sana’o’i, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma bunƙasa tattalin arziki.
An bayyana hakan ne a yayin taron shekara-shekara karo na biyu na kwamitin shugabannin kwalejojin Ilimi, wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar kula da kwalejojin Ilimi ta ƙasa (NCCE) da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labarai da tsare-tsare, Dahiru Gurama ya fitar, ƙaramin ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmad, ta jaddada cewa lokaci ya yi da kwalejojin ilimi za su wuce koyar da darussan aji kawai, su karkata zuwa horas da ɗalibai sana’o’i domin su dogara da kansu tare da samar da ayyukan yi.
Ta ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na da ƙudirin ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci a fannin horas da malamai.
A nata ɓangaren, Babbar Sakatare ta NCCE, Dokta Angela Ajala, ta bayyana cewa haɗa koyon sana’o’i cikin tsarin koyarwa na da matuƙar muhimmanci wajen samar da malamai masu ƙwarewa da kuma dogaro da kai.
Shi ma shugaban kwamitin shugabannin kwalejojin Ilimi, Dokta Ali Adamu, ya ce taron ya bai wa mahalarta damar tattauna manyan ƙalubalen da ke addabar fannin tare da samar da hanyoyin magance su.
Taron ya kuma samu wani ɓangare na musamman inda aka karrama tsohon Babban Sakatare na NCCE, Farfesa Okwelle Paulinus Chijioke, bisa rawar da ya taka wajen bunƙasa ilimin malamai a ƙasar nan.
Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabo, Farfesa Okwelle ya gode da wannan karramawa, tare da alƙawarin ci gaba da bayar da gudunmawa wajen cigaban ilimi da horas da matasa.
Haka kuma, an gudanar da liyafar bankwana ga wasu shugabanni 32 da suka yi ritaya ko ke shirin barin aiki, inda aka jaddada muhimmancin haɗin kai da ɗorewar ƙoƙarin domin inganta ilimin malamai da kuma bunƙasar kasa baƙi ɗaya.
