Farfesa Abdallah Uba Adamu: Shekaru 70 na ilmi, bincike da sauya tarihi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

A ranar 25 ga Afrilu, 2026, al’ummar ilimi a Nijeriya, musamman na Jami’ar Bayero da ke Kano, sun yi wa wani babban gwarzon ilimi bankwana na kammala aiki bayan sama da shekaru 40 yana koyarwa, bincike da jagoranci.

Ritayar Farfesa Abdallah Uba Adamu ba kawai ƙarshen aikin gwamnati ba ne, a’a wata muhimmiyar alama ce ta cika tafiyar rayuwa mai cike da hidima ga ilimi, al’adu da cigaban al’umma.

A tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama ɗaya daga cikin fitattun malaman jami’a da suka haɗa ilimin kimiyya da na zamantakewa wuri guda. Wannan ne ya sa aka san shi a matsayin “Farfesa biyu a ɗaya,” kasancewar ya zama farfesa a fannoni biyu mabambanta — Science Education a 1997 sannan kuma a Media and Cultural Communication 2012.

Wannan nasara ta sanya shi cikin ƙalilan ɗin da suka kafa tarihi irin wannan a Nijeriya baki ɗaya, domin shi kaɗai ne a arewacin Nijeriya da ya samu wannan nasara yayin da ya zama mutum uku ne kacal a Nijeriya.

Rayuwa mai cike da Ilimi

An haifi Farfesan a unguwar Daneji da ke Kano a shekarar 1956, cikin gida mai cike da sha’awar ilimi da tarihi. Mahaifinsa, marigayi Uba Adamu, shahararren masanin tarihi ne wanda ya taka rawa wajen gina tushen son ilimi a rayuwarsa. Daga karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello zuwa manyan jami’o’i irin su University of London da University of Sussex, rayuwarsa ta kasance tafiya ta neman ilimi da bincike.

Amma a Jami’ar Bayero Kano ne ya fara gina sunan da ya zama abin alfahari ga Arewacin Najeriya tun daga shekarar 1981.

Duk da manyan mukamai da lambobin yabo da ya samu, abin da ya fi bayyana Farfesa Abdallah Uba Adamu shi ne yadda ya sauya rayuwar mutane ta hanyar ilimi. Dalibai da dama na kallonsa a matsayin malami mai ƙarfafa tunani da buɗe ƙofofin nasara.

A wajensa, aji ba wurin koyarwa kawai ba ne, wuri ne na gina tunani da wayar da kai. Abokan aikinsa kuma sun san shi a matsayin mutum mai natsuwa, tsari da sauƙin kai.

Bunƙasa harshen Hausa

Baya ga aikin koyarwa, Farfesan ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa harshen Hausa da kuma nazarin al’adun Hausawa. A shekarun 1990, ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da haruffan Hausa masu lanƙwasa kamar ɓ, Ɓ ɓ, ɗ, Ɗ, da ƙ a tsarin kwamfuta a shekarar 1990 wani abu da ya taimaka wajen bunƙasa rubutun Hausa a duniyar zamani.

Sauya fasalin Kannywood

Haka kuma Farfesa Abdullah ya yi fice wajen nazarin fina-finan Hausa, inda ya taimaka wajen ɗora masana’antar Kannywood a taswirar binciken fina-finai na duniya.

A lokacin da ake kallon Kannywood a matsayin nishaɗi kawai, Farfesa Adamu ya fito da bincike da rubuce-rubuce da suka nuna cewa masana’antar tana ɗauke da tarihi, al’adu da sauye-sauyen zamantakewar al’umma. Ta haka ne ya taimaka wajen sanya Kannywood cikin sahun masana’antun fina-finai da ake nazari a kansu kamar Nollywood da Bollywood.

Tasirinsa a ba a iya aji ba ne

Tasirin Farfesan bai tsaya a cikin jami’a kawai ba. A matsayinsa na tsohon shugaban National Open University of Nigeria tsakanin 2016 zuwa 2021, ya jagoranci sauye-sauye masu yawa a tsarin karatun nesa tare da faɗaɗa damar samun ilimi ga dubban ɗalibai a faɗin ƙasar nan.

A lokacin shugabancinsa ne jami’ar ta samu karɓuwa sosai musamman a Arewacin Najeriya, inda jihar Kano ta kasance daga cikin jihohin da suka fi yawan ɗalibai.

Ko da yake ya kai wannan matsayi na ƙwarewa da ƙima, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kasance mutum mai barkwanci da kusanci da jama’a. Yakan yi hulɗa da matasa a kafafen sada zumunta, yana ba su shawara tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen neman ilimi da cigaba. Mutane da dama sun shaida yadda yake sauraro cikin natsuwa tare da bayar da shawarwari masu amfani.

Shekaru 70 masu albarka

A yau da ya cika shekaru 70 tare da yin ritaya daga aikin jami’a, mutane da dama na ganin cewa wannan ba ƙarshen gudummawarsa ba ne. Maimakon haka, wata sabuwar dama ce ta ci gaba da rubuce-rubuce, bincike da bayar da gudummawa ga ci gaban ilimi da al’umma ba tare da takurawar aiki ba.

Ko a kasashen Inyamurai sun bashi lambar yabo da sarauta iri-iri a lokacin da yake shugabancin jami’ar karatu daga gida wato Open University.

Hakika, tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu ya wuce labarin mutum guda. Labari ne na sadaukarwa, ƙwazo da kishin ilimi. Ya kasance cikin mutanen da ba wai kawai suka bi tarihi ba, sun taimaka ne wajen sauya shi.

Kuma duk inda ake magana kan ilimi, al’adu da cigaban Hausawa a Nijeriya da duniya sunansa zai ci gaba da kasancewa cikin jerin waɗanda suka bar gado mai ɗorewa.

By ukarofi