Daga JOHN D WADA a Lafia
Ƙungiyar yaƙin neman nasarar ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa Sanata Aliyu Ahmed Wadada a Tudun-Gwandara da ake kira Tudun-Gwandara For Wadada Vision 2027 a turance sun gudanar da babban taron buɗe sabon ofishin kamfen na yankin tare da karɓar dinbin magoya bayan ‘yan takarar gwamnan da suka janye suka dawo tafiyar Wadada a yankin.
A jawabinsa na maraba a wajen taron shugaban tafiyar Wadada a Tudun-Gwandara Comrade Mohammed Maihadishi ya marabci duka waɗanda suka halarci taron dama waɗanda basu samu damar zuwa ba inda yace ƙungiyar Tudun-Gwandara For Wadada Vision 2027 ta shirya taron ne da manufar karɓar wasu magoya bayan wasu ‘yan takarar gwamnan jihar daban da suka dawo tafiyar Wadada daga wasu sassan jihar da buɗe sabon ofishin kamfen na Wadada a Tudun-Gwandaran da kuma bai wa masu canja shekar takardun aiki da sauransu.
Ya bayyana kyawawan halayyar Sanata Aliyu Ahmed Wadada inda yace tabbas shine kawai ya dace ya gaji Gwamna Abdullahi Sule a kujerar gwamnan inda ya yi kira na musamman ga al’ummar yankin na Tudun-Gwandara da jihar Nasarawa baki ɗaya su tabbatar sun fito kwansu da kwarkwata su zaɓi Sanata Wadada don zama gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Comrade Mohammed Maihadishi daganan ya jaddada cewa tafiyar ta Sanata Aliyu Ahmed Wadada tafiya ce ta gaskiya tafiya ce kuma ta arzikin inda ya ƙara? da cewa ba shakka duk wanda yayi Wadada ba zai yi dana-sani ba amma duk wanda bai yi shi ba zai yi nadama daga bisani.
Sauran manyan baƙi ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a tafiyar ɗan takarar kujerar gwamnan da suka halarci taron suka kuma yi jawabi da suka haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan jihar wato Sanata Musa Sambo da Alhaji Baba Wakilin Dokan Lafia da wasu ƙungiyoyin yaƙin nasarar Sanata Aliyu Ahmed Wadada daban-daban da sauransu duk sun yaba wa hangen nesa da ƙungiyar Tudun-gwandara For Wadada Vision 2027 din suka yi na haɗa taron inda suma suka bayyana zaɓin da gwamnatin jihar ta yi akan Wadada ne ɗan takarar ta a matsayin zabi nagari kana suka yi kira ga ɗimbin magoya bayansa anan Tudun-gwandara da jihar baki daya su shigo ayi tafiyar dasu.
Sun kuma yi alƙawarin shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo don tabbatar Wadada yayi nasara a zaɓen fit da gwanin APC dake tafe da kuma na gama-gari a 2027.
Har ila yau manyan ‘yan siyasan sun yaba wa mataki da waɗanda suka bar ‘yan takarar nasu suka shigo tafiyar Wadada din suka ɗauka inda suka ce tabbas sun ɗauki kyakkyawar mataki.
Sauran abubuwa da aka gudanar a yayin taron sun haɗa da gabatar da satificate na kama aiki wa ɗimbin magoya bayan ‘yan takarar da suka dawo yin Wadada din wanda Sanata Musa Sambo yayi a hukumance da ƙaddamar da sabon ofishin yaƙin neman zaɓen Wadada din na Tudun-gwandara da ɗaukan hotuna da sauransu inda su kuma anasu ɓangaren makada da mawaƙa suka nishaɗantar da jama’a.
