Yadda bashin Nestoil ya jefa bankunan Nijeriya cikin ƙalubale

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fargaba na ƙaruwa a fannin bankunan Nijeriya bayan da wasu manyan bankuna uku suka gaza sanar da ribar masu hannun jari a sakamakon shekarar kuɗi ta 2025, sakamakon tarin basussuka masu nauyi, inda kamfanin mai na cikin gida, Nestoil Limited, ke da kusan bashin Naira tiriliyan 2.9.

Masana na ganin wannan lamari na nuna wata babbar jarrabawa ga tsarin bankunan ƙasar, musamman a daidai lokacin da ake aiwatar da tsarin gyaran lissafin kuɗi.

Daga cikin bankunan da lamarin ya fi shafa akwai United Bank for Africa (UBA) da Access Bank, waɗanda ba su fitar da ribar masu hannun jari ba. Rahotannin kuɗi sun nuna cewa UBA ya ware naira biliyan 331 domin asarar lamuni, yayin da Access Holdings ya ƙara yawan asarar lamuni da kashi 209 zuwa naira biliyan 287.3.

A ƙarshen 2024, bankunan Nijeriya sun zuba sama da naira tiriliyan 21 a fannin mai da iskar gas, inda bankunan da suka fi fuskantar haɗari daga bashin Nestoil suka haɗa da First Bank of Nigeria, FCMB Group, Ecobank da kuma Afreɗim Bank.

A ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, an hana bankunan da abin ya shafa biyan riba har sai sun kammala tanadin asarar basussukan da ba a biya, wato Non-Performing Loans (NPL).

Wannan tsauraran mataki ya jawo asarar kuɗi har Naira tiriliyan 2.16 a cikin manyan bankuna biyar, wanda hakan ya rage ribar da suka samu, tare da hana su raba riba ga masu hannun jari.

Asalin rikicin ya ta’allaƙa ne da gazawar Nestoil wajen biyan basussukan haɗin gwiwa, wato syndicated loans, waɗanda aka bayar lokacin da ake sa ran samun ƙaruwar samar da mai. Rashin biyan bashin ya jefa bankuna cikin matsin lamba, musamman waɗanda suka fi zuba jari a fannin mai da iskar gas.

A wani mataki na shari’a, bankuna sun samu umarnin kotu na Mareva a watan Oktoban 2025, wanda ya sa aka kulle kadarorin kamfanin, ciki har da kuɗaɗen asusu, kadarori da kayayyakin mai a cibiyoyi sama da 20. Duk da haka, ana ci gaba da shari’o’i tsakanin ɓangarorin.

Yanzu haka bankuna na ƙoƙarin kwace kadarori domin dawo da bashin, lamarin da ka iya jawo dogon rikicin shari’a da kuma rage yawan kuɗaɗen da ke zagayawa a tsarin banki. FCMB Group ta ninka asarar lamuni zuwa naira biliyan 92.5, yayin da FirstHoldCo Plc ya fuskanci asarar naira biliyan 748 saboda matsin lambar da CBN ya sa wajen bayyana basussukan da ba a biya. Ecobank Group ma ya samu asarar lamuni mai yawa da ya kai naira biliyan 707.52, yayin da Access Holdings ya ga ribarsa ta ragu da kashi 58, lamarin da ya sa ya dakatar da raba riba.

Masana sun gargaɗi cewa dawowar bankunan daga wannan hali na iya ɗaukar lokaci. Sabon tsarin CBN ya fi mayar da hankali kan riƙe jari, inda aka tanadi cewa ba za a biya riba ba har sai NPLs sun sauka ƙasa da kashi 5.

A shekarar 2025, adadin NPL ya kusa kai kashi 7, abin da ke nuna barazana ga daidaiton bankuna idan matsalolin basussukan mai suka ci gaba. Sai dai masana na ganin wannan tsauri na CBN na da muhimmanci domin kauce wa sake faɗuwar tsarin banki irin na shekarar 2009, ta hanyar tilasta bankuna su bayyana asararsu a fili maimakon ɓoye ta.

A ƙarshe, ana kallon wannan yanayi a matsayin wata muhimmiyar mataki na sake gina ƙarfi da gaskiya a fannin bankunan Nijeriya, duk da wahalar da yake jawo wa masu zuba jari a halin yanzu.

By ukarofi