Jiragen ruwa maƙare da fetur da abinci za su iso Nijeriya – NPA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) ta sanar da ana sa ran jiragen ruwa guda 36 ɗauke da kayayyaki daban-daban, ciki har da man fetur da kayan abinci, za su isa manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a rahoton ta na yau da kullum mai taken “Daily Shipping Position”, NPA ta bayyana cewa jiragen za su sauka ne a tashoshin Apapa Port, Lekki Deep Sea Port da kuma Tin Can Island Port tsakanin ranar 5 zuwa 10 ga watan Mayu.

Hukumar ta ce daga cikin jiragen da ake sa ran isowarsu, guda 15 na ɗauke da kwantena masu ɗauke da kayayyaki iri-iri, yayin da sauran guda 21 ke ɗauke da kayan masarufi da suka haɗa da kifin sabo, kaya na gama-gari, man jiragen sama, alkama, man dizel, fetur, da kuma ɗanyen mai.

NPA ta ƙara da cewa a halin yanzu, jiragen ruwa guda 11 da tankokin mai sun riga sun iso waɗannan tashoshi, inda suke jiran samun damar sauke kaya kamar kwantena, taki, fetur, man gas da sauran kayayyaki.

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa jiragen ruwa guda 24 na ci gaba da sauke kayayyaki a tashoshin uku, ciki har da taki, alkama, kwantena, kifin sabo, man jiragen sama da dizal.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin tabbatar da wadatar kayayyaki a ƙasar, musamman man fetur da kayan abinci, domin rage matsin tattalin arziki da kuma inganta harkokin kasuwanci.

By ukarofi