Amnesty ta yi Allah-wadai da bangar siyasa a Kano, ta buƙaci a binciki kisan mutane biyar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta buƙaci hukumomin Nijeriya da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan wasu mutane biyar da ake zargin wasu ‘yan daba masu dauke da makamai sun kai musu hari a jihar Kano.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta yi Allah-wadai da lamarin tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan tashe-tashen hankulan siyasa da aka samu a jihar Kano cikin ‘yan shekarun nan.

A cewar ƙungiyar, lamarin ya faru ne ranar Talata 5 ga watan Afrilu, 2026, inda ta ce hare-haren na nuna yadda rikice-rikicen siyasa ke kara kamari tare da zama barazana ga rayuka da harkokin dimokuradiyya.

Amnesty International ta ce wasu bidiyoyi da ta samu daga wurin da lamarin ya faru sun nuna yadda wasu gungun mutane dauke da makamai suke bin wasu mutane da suka rika gudu kafin daga bisani su kai musu munanan hare-hare.

Kungiyar ta kara da cewa an ga wasu daga cikin wadanda aka kai wa harin kwance cikin jini yayin da suke kokarin neman taimako domin tsira da rayukansu.

A cewar ƙungiyar, ana zargin maharan sun sanya rigunan da ke dauke da tambarin jam’iyya mai mulki, yayin da ake jin suna furta kalaman barazana da tashin hankali a lokacin harin.

“Wannan na daga cikin mafi munin tashin hankalin daba da aka samu cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan,” inji Amnesty International.

ƙungiyar ta bukaci hukumomin Nijeriya da su gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da an gano wadanda suka aikata laifin da kuma duk wasu ‘yan siyasa da ake zargin suna daukar nauyin irin wadannan kungiyoyi.

Ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu kungiyoyin ‘yan daba masu alaka da fitattun ‘yan siyasa ke kara zama barazana ga rayuka, dukiyoyi da ‘yancin jama’a na gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.

Amnesty International ta ce ci gaba da rashin hukunta masu hannu a irin wadannan laifuka na ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen aikata ta’addanci da tada zaune tsaye musamman a lokutan siyasa.

“Wannan lamari yana nuna yadda rikice-rikicen siyasa masu hadari ke kara yawaita a jihar Kano cikin watannin baya-bayan nan,” inji ƙungiyar.

Ta ƙara da cewa wasu ‘yan daba masu dauke da makamai da ake zargin suna aiki wa wasu manyan ‘yan siyasa suna kara zama barazana ga hakkin rayuwa, inda suke gudanar da ayyukansu tamkar suna da cikakken kariya daga hukuma.

ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya, shugabannin siyasa da jam’iyyun siyasa da su tabbatar da bin doka da oda tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a kafin, lokacin da bayan gudanar da harkokin siyasa.

Haka kuma ta jaddada muhimmancin hukunta duk wadanda aka samu da hannu a irin wadannan hare-hare domin dakile ci gaba da tashe-tashen hankulan siyasa a gaba.

Zu zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da zarge-zargen da Amnesty International ta yi ba.

By ukarofi