Kotu ta bai wa El-Rufai izinin zuwa jinya a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun tarayya da ke Kaduna ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, izinin zuwa neman maganin haƙori da ido a wasu asibitoci da ke Abuja ƙarƙashin kulawar jami’an ICPC.

Mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Okor Odey, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce lauyan El-Rufai ya roƙi kotu da ta umurci ICPC ta ba wanda ake tuhuma damar samun kulawar lafiya.

Kotun ta umurci ICPC da ta riƙa raka El-Rufai zuwa asibitocin da ya zaɓa, ciki har da Mile Dental Clinic da Skipper Eye-ƙ Hospital da ke Abuja, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, tare da dawo da shi wurin da ake tsare da shi bayan an kammala jinya.

Haka kuma, kotun ta jaddada cewa duk wata tafiya za ta kasance ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro da cikakken kulawar ICPC.

A baya dai ICPC ta gurfanar da El-Rufai bisa zarge-zargen damfara da wanke kuɗi, sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

A watan Afrilu, kotun ta ba shi beli kan kudi naira miliyan 200 tare da mutum biyu da za su tsaya masa.

Sanarwar ta ƙara da cewa zaman kotun na ranar Laraba ya mayar da hankali ne kan buƙatar El-Rufai na sauya wasu daga cikin sharuɗɗan belin da aka ba shi a baya.

Bayan sauraron hujjojin lauyoyi, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga Mayu domin yanke hukunci.

By ukarofi