
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta yi gargadin cewa aƙalla jihohi 19 a fadin Nijeriya ka iya fuskantar ambaliyar ruwa acikin kwanaki masu zuwa sakamakon dakon mamakon ruwan sama da ake sa ran samu.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, NiMet ta bayyana cewa, haɗarin ambaliya ya ƙaru saboda bushewar kasa da zai hana ruwa ya ratsata yadda ya kamata, wanda hakan zai haifar da ka iya haifar da ambaliyar.
Hukumar ta ce Jihohin da abin zai shafa sun hada da Zamfara, Nasarawa, Kwara, Oyo, Legas, Ogun, Ekiti, Delta, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Edo, Ondo, da kuma Bayelsa.
A cewar hukumar, illar da ambaliyar ruwan za ta iya haifarwa sun hada da ambaliyar ruwa, hana zirga-zirgar ababen hawa, lalata gidaje, gonaki, da muhimman ababen more rayuwa, toshe hanyoyin magudanan ruwa, katsewar wutar lantarki, da katsewar hanyoyin sadarwa, da kuma kara hadarin cututtuka da su ka shafi ruwa.
NiMet ta shawarci mazauna yankunan da abin zai shafa da su ɗauki matakan da su ka dace ta hanyar share magudanun ruwa da su ka toshe a kusa da gidajensu, tare da bin sharwarwarin hukumomi da ke faɗakarwar kan ambaliyar ruwa.
Hukumar ta kuma gargadi masu ababen hawa da masu tafiya a kasa da su guji tuki ko tafiya ta wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa.
Ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su karfafa hadin kai, da shirye-shirye, da hanyoyin ba da agajin gaggawa domin dakile hadurran da ke da alaka da ambaliya.
Wannan gargadin na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta sanar a kwanakin baya cewa al’ummomi 14,118 a jihohi 33 da kuma babban birnin tarayya Abuja na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a shekarar 2026.
