
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya ce duk wanda ya kashe mutumin da ba shi da laifi yana kabbara (Allahu Akbar), to wuta ce makomarsa.
Ya jaddada cewa addinin Musulunci bai koyar da hakan ba, kuma babu dalilin karkashe mutane da sunan addini.
Sarkin ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin taron Majalisar Tattaunawa Tsakanin Addinai ta Ƙasa (NIREC) da aka gudanar a Abuja.
Ya buƙaci al’umma da su daina danganta ta’addanci da addini, inda ya ce “Bari mu kira su da sunansu na asali—masu laifi. Kada a ce masu laifi Musulmai ko ’yan ta’adda Musulmai.”
Muhammadu Sa’ad ya ƙara da cewa jin yaren Larabci ba ya mayar da mutum malamin addini, domin Larabci yare ne kawai, kuma jahilci ne ke sanya mutane karkashe wasu.
Haka kuma, ya yi gargadin cewa masu tayar da boma-bomai a kasuwanni suna kabbara za su sha wahala a gidan gaskiya saboda ɗaukar ran da Allah ya haramta haramun ne.
Wannan bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da wani bidiyo ya karaɗe gari na wani ma’aikaci a Ado-Ekiti, wanda aka ji yana barazanar kashe duk wanda ya zagi Annabi Muhammad (SAW), yana mai iƙirarin cewa yin hakan zai kai mutum gidan Aljanna kai-tsaye.
Sarkin ya yi watsi da wannan ra’ayi, inda ya ce hakan ya saba wa koyarwar addinin Islama.
