
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya OSGF, ya yi gyara akan salon gabatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu biyo bayan kurakurai da ake samu daga ɓangaren ‘yan jarida dangane da al’amarin.
Mai ba wa sakataren gwamnatin shawara akan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a yau Juma’a.
Ya ce, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne ya yi gyaran musamman domin ankarar da fannin jarida da ɗaukacin al’umma akan batun.
A cewarsa, Akume ya roƙi al’umma da gidajen jarida da su riƙa tantance laƙabi a hukumance gabanin wallafawa domin kauce wa abin da ya kira da da “tozarci da kurakurai da za a iya kauce musu”.
Ya bayyana cewa, salon gabatar da shugaban a hukumance shi ne: “‘His Excellency, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, President and Commander-in-Chief of the Armed Forces, Federal Republic of Nigeria'”, inji shi, wato ‘Mai Girma, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Shugaba kuma Kwamandan Rundunonin Tsaro, Tarayyar Nijeriya’.
Odunuga ya kuma shawarci da a riƙa ziyartar sahihan shafukan OSGF na dandalin Facebook, Instagram, X da kuma Imel – [email protected] domin samun ainihin yadda salon yake a hukumance.
Kazalika, Odunuga ya bayyana cewa, Akume ya ce za a iya kauce wa kuren cikin sauƙi ta hanyar amfani da tantancewa ta shafukan kafin wallafawa.
