‘Yan sandan Nasarawa sun cafke masu garkuwa da mutane

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama mutum takwas da ake zargi da garkuwa da mutane sannan ta kashe mutum ɗaya cikinsu yayin wani sintiri na musamman da jami’an suka gudanar jim kaɗan da samun labarin garkuwa da mutanen.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Nasarawa Mohammed Shatima Jauro ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a ofishin sa dake Lafia.

Ya bayyana rahoto kan wannan gagarumin nasara da rundunar ta samu a yaƙi da masu garkuwa da mutanen da sauran laifuffuka masu tashin hankali a jihar.

Kwamishina Shatima Mohammed Jauro ya ce saurin amsawa da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaron jihar ne suka kai ga kama mutum takwas da ke da hannu a aikata ɗanyen aikin inda aka kashe mutum ɗaya cikin mugayen mutanen.

Kwamishinan ya kuma bayyana sunayen waɗanda aka cafken cewa sun hada da Adamu Alfa mai shekara 35 da Muhammed Alfa 25 da Shuaibu Alfa 33 da Usman Alfa 25 da Ali Alfa 30 da Isa Alfa 15 da Adamu Alfa 25 da Kuma Ja’afaru Alfa shekaru 38. Kuma dukkan waɗanda ake zargin ‘yan Rugan Alhaji Alfa ne dake ƙauyen Rukubi a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan Mohammed Shatima Jauro ya cigaba da bayyana cewar “A ranar 7 ga Mayu na 2026 da kusan ƙarfe 1:00 na safe mun samu rahoto daga jami’anmu da ke kula da ofishin Rukubi ta hannun jami’in ‘yan sanda na Ekye Division cewa a ranar 6 ga Mayu 2026 kusan karfe 10:30 na dare wasu ‘yan daba ɗauke da muggan makamai sun farmaki ƙauyen Rukubi a ƙaramar hukumar Doma anan jihar Nasarawa suna harbi ba kakkautawa kuma suna jefa mazauna cikin tsoro,” in ji shi.

Ya ƙara cewa yayin harin ‘yan ta’addan sun shiga gidajen Habib Usman da Peter Ajidiku inda suka sace mutum biyu da ake kira Ayele Jonathan da Rose Samuel suka tafi da su wani wuri da ba a sani ba.

“Da samun wannan rahoto gaggawa sai muka tura tawagar ‘yan sandanmu wurin nan da nan tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya da ƙungiyar tsaro ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) da National Forest Security Service (NFSS) da matasan yankin da ke faɗakarwa,” in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa yayin aikin an ƙwato bindigogi nau’in AK-47 guda biyu da babura nau’in Bajaj guda huɗu daga hannun waɗanda ake zargi sannan an samu harsasai biyu na AK-47 da aka harba a gidan waɗanda aka sacen a matsayin shaida.

“Haka kuma ɗaya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Muhammed Alfa ya samu munanan raunuka yayin faɗa da jami’an tsaro inda daga baya ya rasu yayin da ake yi masa magani,” in ji shi.

Ya bayyana wannan nasara a matsayin shaida kan yadda haɗin gwiwar hukumomin tsaro ke aiki da kuma jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane a fadin jihar Nasarawa.

Ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tsarkake jihar baki ɗaya daga ‘yan ta’adda da tabbatar da cewa duk wanda ke da hannu a garkuwa da mutane da tashin hankali ya fuskanci fishin jami’an rundunar da kuma shari’a.

Sannan a ƙarshe ya roƙi jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da bayanai masu inganci akan lokaci domin haɗin kai tsakanin jama’a da tsaro shi ne mabuɗin yaki da laifi.

By ukarofi