Filato: ‘Yan bindiga sun halaka mutum 13 da raunata da dama a sabon hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a Jihar Filato, sun halaka kimanin mutane 13 a ƙauyen Ngbra Zongo da ke Gundumar Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa.

Al’amarin ya auku ne a safiyar ranar Juma’a, wanda ya jefa al’umma cikin firgici kuma ya yi sanadiyyar raunata mutane da dama.

Wani mazaunin yankin mai suna Philip Alanga ya shaida wa ‘yan jarida a Jos cewa maharan sun farmaki ƙauyen ne da tsakar dare, inda suka yi ta harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi kana suka riƙa saran su da adduna da wasu makamai masu haɗari.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun riƙa shiga gida-gida suna farmakar waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, inda suka halaka wasu da raunuta wasu masu yawa.

Ya ƙara da cewa, ganin haka ya sa mutane da dama suka riƙa tserewa zuwa bayan gari domin tsira da rayukansu, lamarin da ya sa wasu suka jikkata da neman agajin kula da lafiyarsu.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Babban Sakataren Ƙungiyar Ci-gaban Al’ummar Irigwe (IDA), Mista Ɗanjuma Auta, ya bayyana harin a matsayin abin da aka yi cikin rashin tausayi da kuma suke alla-wadai da shi.

Ya kuma ce, ire-iren harin na faruwa a ƙauyukan ƙaramar hukumar da wasu sassan Filato, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ba rayuka da dukiyoyin al’ummomin jihar kariya.

By Babaji