Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sabon Ajiyan Kano, Muhammadu Sanusi Bello, da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ya naɗa a fadarsa ranar Juma’a, ya bayyana cewa yana cikin farin ciki mara misaltuwa da naɗin da aka yi masa, wanda a cewarsa wata alama ce ta yarda da kuma karramawa a gare shi.
Da yake zantawa da manema labarai, ya ce duk wanda ya je wajen naɗin ya ji irin jawabai da sarki ya yi musamman a kansa na yabo da kuma bayyana dalilan naɗa shi sarautar Ajiyan Kano, ya san cewa wannan kyakkyawar shaida da sarki ya yi masa ta fi masa daɗi fiye da sarautar kanta.
Ajiyan Kano ya ƙara da cewa ba shi kaɗai ba ne hakimin sarki a Kano, su 74 ne, amma aka zaɓe shi aka ce shi ne Ajiyan Kano, wanda ya bayyana a matsayin babbar nasara da farin ciki da bakinsa ma ba zai iya bayyanawa ba. Ya ce abin da ya rage musu shi ne su ci gaba da yi wa sarki addu’a, Allah ya tsare mutuncinsa, ya dawwamar masa da nasara da rinjaye, ya ƙara masa lafiya da dogon kwana.
Ya ƙara da cewa wannan sarauta ta Ajiya ba a ba wa wanda ba a aminta da shi ba, don haka duk wanda sarki mai daraja irin na Kano ya ba wannan sarauta, akwai tabbacin yana da yarda, aminci, amana da riƙon gaskiya.
Ajiyan Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Bello, ya ce a tarihin Kano ba a saba da sarautar Ajiya ba a da, sai dai marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, shi ne ya fara ƙirƙirar sarautar, inda aka naɗa Alhaji Muhammadu Dansarari wanda ya rasu, daga bisani ɗansa Aminu Dansarari ya gaje shi. Daga nan kuma sai aka naɗa shi, inda ya gaji Ja’afar Shanono. A cewarsa, idan aka yi la’akari da tsarin lissafi, an yi sarautar Ajiya guda uku kafin nasa, shi ne na huɗu a saninsa.
