Daga AISHA ASAS
A duniyar fina-finan akwai labaran da lokaci ba ya iya share su. Daya daga cikin su shi ne rikicin soyayya tsakanin Ross da Rachel a cikin shahararren shirin barkwanci nan da duniya ta yi amo da shi, wato ‘Friends’ rikicin da ya haifar da sanannen mai cike da ce-ce-ku-ce, wato “We were on a break.”
Shekaru kusan talatin kenan, amma har yanzu waɗannan kalmomi guda uku na ci gaba da raba kan masoya shirin, inda wasu ke ganin hujja ce, wasu kuwa na ganin uzuri ne. Tsayin shekaru ana ja-ni-in-ja ka kan wannan muhawarar ta ko hujja ce don sun tafi hutu kamar yadda suka kira abin ya je ya yi abinda ya ga dama.
Tsayin lokaci kafin a samu wannan lamari ya lafa wanda muke tunanin ya tafi da tagomashin shirin. Sai dai hakan bai tabbata na domin jin kaɗan bayan tattaunawa da jarumar shirin, Lisa Kudrow, lamarin ya dawo sabo fill, har kalmomin suka dawo bakunan mutane tamkar dai ba su tafi ba.
Domin fahimtar wannan muhawara, dole ne a koma ga abin da ya faru a cikin labarin. A lokacin, Rachel (Jennifer Aniston) ta fara sabuwar rayuwa mai cike da ƙalubale a aikinta, wanda ya sa ta kasance cikin matsin lamba da rashin samun lokaci sosai ga soyayyarta da Ross (David Schwimmer).
Ross kuwa, maimakon ya fahimci halin da take ciki, sai ya fara nuna damuwa da rashin amincewa, har ya kai ga rashin jituwa mai tsanani tsakaninsu.
A cikin musayar yawu da ya tsananta, Rachel ta furta cewa ya dace su ɗan dakatar da dangantakar, wato su ba juna sarari na wani lokaci. Wannan shi ne tushen kalmar “on a break” ba wai rabuwa ta dindindin ba, wato dai ɗan kaucewa juna na ɗan lokaci a samu huta don samun damar tantance halin da ake ciki.
Amma abin da ya tayar da ƙura shi ne: cikin dare ɗaya bayan wannan magana, Ross ya tafi ya kwana da wata mace.
Washegari, Rachel ta bayyan cewa, ba ta ɗauki abin a matsayin cikakkiyar rabuwa ba, amma Ross ya dage cewa ai suna kan “hutu” ne, don haka bai aikata laifi ba. Daga nan ne aka haifi muhawarar da ta ƙi mutuwa.
Lokacin da Lisa Kudrow ta bayyana a shirin ‘The Tonight Show’ tare da Jimmy Fallon, an sake jefa wannan batu a gaba, amma abin da ta faɗa ya sauya yanayin tattaunawar gaba ɗaya.
Da farko ta nuna shakku, kamar mai jin tsoron sake tayar da tsohon rikici. Amma daga bisani ta yanke hukunci faɗar albarkacin bakinta a karo na ba adadi tun faruwan wannan ɓangare a shirin.
“Bai kamata muhawarar ta tsayu kan suna hutu ne ko akasin haka ba, magana ta gaskiyar ita ce Ross bai kasance saurayi nagari ba.”
Wannan furuci nata ya girgiza masu sauraro, inda suka amsa da tafi da goyon baya, alamar cewa mutane da dama sun fara karkata zuwa wannan sabon fahimta.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda Kudrow ta bayyana cewa a baya, har su kansu ‘yan wasan sun fi karkata ga goyon bayan Ross.
Ta tuna cewa a lokacin taron haɗuwar su na baya, sun ɗauki Rachel a matsayin wadda ta ɗauki abin a matsayin babba alhali yana ƙarami. Amma yanzu, bayan shekaru da gogewa, ta ce ta fahimci cewa matsalar tana wurin Ross ne domin ba a yi tsayin lokacin da ya kamata a ce ya fara cin amanar ta ba.
A cewarta, abin tambaya ba wai Ross ya kwana da wata mace ba ne kawai, yadda ya kasa jure ɗan lokaci na rashin kulawa daga budurwarsa, wadda ke fama da matsin lamba a rayuwar aikin da ta fara.
Duk da wannan sabon matsayi, sauran jaruman ba su sauya ra’ayinsu ba. Domin Ross ya daɗe yana cewa babu wata shakka sun kasance a hutu ne shi ya sa ya aikata abinda ya yi. Ita kuwa Jennifer Aniston ta tsaya kan ra’ayinta na ya ci amanarta
Wannan bambanci ya tabbatar da cewa wannan muhawara ba wai kawai labari ba ne, ta zama wani ɓangare na tarihin talabijin da al’adun masu kallo.
Sabon ra’ayin Lisa Kudrow ya sauya tambayar daga: “Shin suna kan hutu ne?” zuwa “Shin Ross ya nuna halayen da suka dace da soyayya ta haƙiƙa?”
Wataƙila wannan tambayar ce ta sake dawo da muhawarar sabuwa fil har ma ana gogoriyo wurin sake mallakar shirin ga waɗanda suka kalla, yayin da ya ƙara samun tagomashi ta hanyar samun matasa da suka nuna sha’awar kalla don ganin mene ne ke cikin wannan shiri da ya sace zukatan masu kallo tsayin shekaru.
