Mata da yara da dama sun mutu a Zamfara sakamakon harin sojoji

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa sama da mutum 72 ne ake zargin sun rasa rayukansu bayan wani harin sama da sojoji suka kai ya afkawa kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a ranar Lahadi. Wasu majiyoyi sun shaida cewa mata da ‘yan kasuwa na daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su yayin da ake ci gaba da tantance adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka jikkata.

Wani jagoran al’umma mai suna Garba Ibrahim Mashama ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wasu gawarwakin sun lalace matuƙa har ba za a iya gane su ba. Ya bayyana cewa kasuwar Tumfa na karɓar mutane daga wurare daban-daban ciki har da mazauna yankin da kuma ‘yan bindiga, lamarin da ya sanya jama’a cikin halin tsoro da rashin tabbas.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce adadin waɗanda suka mutu ya haura mutum 100, yayin da mutane da dama ke karɓar magani sakamakon raunukan da suka samu. Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa an binne mutum 80 lokaci guda a ɗaya daga cikin ƙauyukan da abin ya shafa, tana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan harin tare da daukar matakan kare fararen hula.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa fararen hula sun mutu a harin. Daraktan yaɗa labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana zarge-zargen a matsayin marasa gaskiya. Duk da haka, rundunar ta ce za ta gudanar da bincike kan lamarin domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.

By ukarofi