Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta tantance adadin ‘yan takarar majalisar dokoki 115 da suka nuna sha’awar tsayawa takara a zaɓen dake tafe a 2027.
Kakakin Jam’iyyar a Jihar Hon. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala tantance yan takarar a Gusau yau Talata.
A cewar sa, hakan ya nuna jam’iyyar tana da ‘yan takarar majalisar dokoki 115 da suke neman kujera 24 dake a majalisar dokokin jihar.
Ya bayyana cewar akwai ƙarin waɗanda har yanzu basu samu halartar tantancewar ba duk da sun sayi form na tsayawa takarar majalisar dokoki a ƙarƙashin Jam’iyyar.
Yana mai nuni da cewar har yanzu kofa a buɗe take ga waɗanda ba a tantance ba, su samu kwamitin tantancewar don a tantance su.
Birnin Magaji ya bayyana tantancewar a matsayin wadda aka gunanar cikin kwanciyar hankali, yana mai jaddada cewa jam’iyyar za ta bai wa kowa damar nuna ra’ayin tsayawa takara a zaɓen da ke tafe.
Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da magoya bayan ta da su cigaba da bada goyon bayan su ga jam’iyyar ta APC don kai wa ga nasara a zaɓen da ke tafe.
“Ya zuwa yanzu, kwamitin tantance yan takarar majalisar dokoki ya samu nasarar tantance yan Ttakara 115, muna jiran sauran waɗanda ba su zo ba su hanzarta don a tantance su.” Birnin Magaji yace
