Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa tsofaffin ‘yan ta’addan da suke cikin shirin gyaran hali da sake mayar da su cikin al’umma ana sanya su yin rantsuwa da Alkur’ani mai girma kafin a kammala shirin nasu. Gwamnatin ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin hana su komawa ayyukan ta’addanci bayan an sake su cikin al’umma.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Zuwaira Gambo, ita ce ta bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na News Central. Ta ce yin rantsuwar da Alkur’ani shi ne mataki na ƙarshe a tsarin gyaran hali na jihar Borno, tana mai cewa duk wanda ya rantse da Alkur’ani ya san girman sakamakon karya alƙawari.
Gambo ta amince cewa har yanzu akwai ‘yan Najeriya da dama da ke nuna shakku kan shirin, saboda tsoron cewa wasu daga cikin tsofaffin mayaƙan za su iya komawa daji. Sai dai ta ce idan hakan ta faru, rayuwarsu za ta shiga haɗari saboda dokokin da ke tafiyar da ƙungiyoyin ta’addanci ba sa yafe wa masu sauya sheka.
Shi ma mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Abdullahi Ishaq, ya bayyana cewa sama da mutum 300,000 ne suka miƙa wuya tun bayan fara rikicin, ciki har da mata da yara da manoma. Ya ƙara da cewa mutane 8,950 ne aka gyara tare da sake mayar da su cikin al’umma a matakai takwas daban-daban, yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a jihar Borno.
