Ku zama jakadun da suka cancanta na NYSC – Gwamna Lawal ga masu hidimar ƙasa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bukaci membobin masu yiwa ƙasa hidima da aka tura jihar da su zama jakadu na gari a yayin da suke yiwa ƙasa hidima a jihar.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin bikin rufe kwas na 2026 na rukunin A Stream II wanda aka gudanar a sansanin horar da matasa na wucin gadi na NYSC, cibiyar horar da malamai ta UBEC, a Gusau.

Gwamna Lawal, wanda sakataren dindindin na ma’aikatar matasa da wasanni, Alhaji Nasiru Galadima Ƙaura ya wakilta, ya shawarci membobin da su kiyaye ɗabi’un alummar da nuna ladabi, tawali’u, da kuma kishin ƙasa.

Ya ƙarfafa musu gwiwa da su bayar da gudummawa mai kyau ga ci gaban al’ummomin da suka karɓi baƙuncin su ta hanyar gudanar da ayyuka masu ƙirƙire-ƙirƙire da ma’ana waɗanda ke da tasiri kai tsaye ga mutane.

“Ku tuna cewa shekarar hidimarku ba wai kawai wajibi ne na ƙasa ba, amma dama ce ta bayar da gudummawa mai ma’ana, bunƙasa kanku, da kuma yin tasiri mai kyau ga rayuwar alummar Jihar Zamfara,” in ji shi.

Gwamnan ya ƙara tabbatar wa membobin cewa jin daɗin su da tsaron su su ne manyan abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba.

Gwamna Dauda ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da yin aiki tare da shugabannin NYSC, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, da shugabannin al’umma don tabbatar da yanayi mai kyau ga membobin NYSC a jihar.

Tun da farko, ko’odinetan NYSC na Jihar Zamfara, Malam Muhammad Lawan Ahmed, ya taya membobin masu yiwa ƙasa hidimar murna bisa nasarar kammala kwas ɗin horon.

Ya roƙe su da su kasance masu himma a wurin aiki kuma su girmama al’adun masu alummar da suka tarar a Jihar.

Ko’odinetan Jihar ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Zamfara da hukumomin tsaro bisa goyon bayan da suka bayar wajen gudanar da aikin horon.

By ukarofi