Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyar ADC ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu, wanda aka kashe bayan sace shi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Laraba, ta ce rasuwar marigayin ta girgiza ta matuƙa, tana mai bayyana shi a matsayin jajirtaccen bawan jama’a mai tawali’u, gaskiya da kishin siyasar ƙasa.
Marigayi Abba Anas Adamu ya wakilci mazaɓar tarayya ta Birniwa/Guri/Kirikasamma a Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011.
Jam’iyyar ta bayyana cewa marigayin ya kasance mutum mai natsuwa da sauƙin kai, wanda ya mayar da hankali wajen kula da muradun al’ummarsa tare da kasancewa kusa da talakawa.
Sanarwar ta ce, rasuwarsa ba rashi ba ne ga iyalansa da al’ummar Jihar Jigawa kaɗai, har ma da ɗaukacin jam’iyyar ADC baki ɗaya.
Jam’iyyar ta kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa da masoyansa juriyar jure wannan babban rashi.
ADC ta ƙara da cewa wannan lamari ya sake bayyana yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a ƙasar nan, lamarin da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
