Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Bayan rantsar da Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano, an samu tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar wasu matasa uku a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa dubban magoya baya ne suka halarci bikin rantsuwar wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Kano cikin cunkoso da annashuwa.
Sai dai bayan kammala bikin ne aka samu hatsaniya tsakanin wasu matasa a yankin Dan Dago, lamarin da ya kai ga rasa rayukan mutane uku.
Wani rahoto daga gidan rediyon Premier ya ce ɗaya daga cikin matasan an kai masa hari ne yayin da yake dawowa daga wurin bikin, inda wasu matasa suka tare shi kusa da titin Race Course suka kai masa farmaki.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi jana’izar matasan uku a makabartar Dan Dolo da ke Kano, duk da cewa hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.
Lamarin ya jawo martani daga jama’a da dama, inda wasu suka bukaci gwamnatin Kano da masu ruwa da tsaki su dauki matakin gaggawa domin dakile yawaitar rikice-rikicen siyasa da tashin hankali tsakanin matasa.
Shugaban masu yada manufofin Sanata Barau Jibrin, Kwamared Adamu Karkasara, ya yi kira ga gwamnati da shugabannin siyasa su hada kai wajen kawo karshen amfani da matasa wajen tayar da tarzoma da rikicin siyasa.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana damuwa kan yadda tarukan siyasa a Kano ke ƙara zama barazana ga zaman lafiya, musamman ganin yadda wasu matasa ke yawo ɗauke da muggan makamai a irin waɗannan taruka.
