Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyun ANPP da PDP, kuma tsohon Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are, Injiniya Bello Sani Gwarzo, ya bayyana cewa duk wata siyasa da yake yi manufarta ita ce samar wa al’umma mafita da inganta rayuwarsu.
Injiniya Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Kano, inda ya ce dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC shi ne saboda halin ƙunci da matsin rayuwa da al’umma ke ciki.
Ya ce ba zai yiwu jama’a na cikin wahala ana kuka da halin matsin rayuwa ba, sannan shugabanni su yi kunnen uwar shegu da koke-koken talakawa.
A cewarsa, shiga jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wani mataki ne na neman samar da sauyi mai anfani ga al’umma.
“Ina siyasa ne domin hidimtawa jama’a da nemo musu mafita. Lokacin da na ga yadda mutane ke fama da matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki, sai na yanke shawarar shiga jam’iyyar adawa domin a samar da gyara,” inji shi.
Da yake magana kan siyasar Nijeriya da yadda jam’iyyun adawa ke kokarin karɓar mulki daga APC, Injiniya Gwarzo ya ce komai yana hannun Allah, wanda yake bayar da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya ga dama.
Ya ce: “Wanda ya bai wa APC mulki a shekarar 2015, idan Ya ga dama zai bai wa wata jam’iyya mulki. A wajen Allah komai mai sauƙi ne.”
Ya kuma bayyana farin cikinsa da yadda mafi yawan magoya bayansa suka ci gaba da kasancewa tare da shi duk inda ya samu kansa a siyasance.
“Ina farin ciki da kusan kashi 80 cikin 100 na magoya bayana suna tare da ni a duk inda na shiga,” ya bayyana.
A ƙarshe, Injiniya Bello Sani Gwarzo ya shawarci matasa da sauran masu son kawo sauyi da su yi rajistar katin zaɓe tare da shiga jam’iyyun siyasa domin zaɓar shugabanni nagari da za su magance matsalolin tsaro, tattalin arziki, noma, lafiya da ilimi a Nijeriya.
