Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar All Progressives Congress APC, a mazaɓar sanata ta Arewa a Jihar Zamfara sun gudanar da wani babban gangami a garin Ƙaura Namoda don nuna goyon bayan yunƙurin Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura na sake zaɓen sa don ⁰komawa Majalisar Dattawa a 2027.
A wurin taron, Ƙaura ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a hukumance, yana mai jaddada aniyar sa don samar wa matasa ayyukan yi sama da 2,000 idan aka sake zaɓar sa.
Ƙaura ya nuna tarihinsa a lokacin wa’adinsa na baya, yana mai cewa an ɗauki matasa sama da 700 aiki ta hanyar wakilcinsa.
Ya yi alƙawarin faɗaɗa wannan ƙoƙarin idan aka sake zaɓar sa.
“Manufata a wannan karon ita ce samar da damar aiki ga matasa sama da 2,000 a gunduma ta Sanata ta Arewa ta Zamfara da kuma jihar baki ɗaya,” in ji shi.
Sanata Ƙaura ya yaba wa shugabannin APC a jihar Zamfara a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal saboda ƙoƙarin da suke yi na ci gaba da haɗin kan jam’iyya.
