Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan bindiga sun sako gawar tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta ƙasa kuma jigo a jam’iyyar ADC, Abba Anas Adamu, bayan da iyalansa suka biya kuɗin fansa har Naira miliyan 50.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace marigayin tare da wani ɗan siyasa daga jihar Jigawa, Ali Tukur Gantsa, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin halartar taron jam’iyyar ADC.
Majiyoyi kusa da iyalan sun shaida cewa masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa, kafin daga bisani aka sasanta aka rage zuwa Naira miliyan 50. An ce kuɗin ne ya tabbatar da sakin Ali Tukur Gantsa, yayin da aka miƙa gawar Anas ga iyalansa.
Lamarin ya jefa mambobin ADC a Jigawa da abokan siyasar marigayin cikin jimami, inda da dama suka bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, tausayi da jajircewa wajen hidimtawa al’umma.
Wata majiya daga cikin iyalan ta bayyana cewa an yi garkuwa da ’yan siyasar biyu ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da suke tafiya daga Kano zuwa Abuja domin wani taron siyasa.
A cewar majiyar, masu garkuwar sun tare su ne a yankin Jere sannan suka tafi da su cikin wani daji da ke kusa da wurin.
“An sace su ne yayin tafiyarsu daga Kano zuwa Abuja domin halartar wani taron siyasa. Da farko masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200, amma bayan doguwar tattaunawa aka amince da Naira miliyan 50,” inji majiyar.
Bincike ya nuna cewa marigayi Anas, wanda ake cewa yana fama da cutar asma da hawan jini, bai samu damar amfani da magungunansa ba a tsawon lokacin da yake hannun masu garkuwa da mutanen.
Majiyoyi sun ce mawuyacin halin da suka shiga, tsoro da damuwar da suka fuskanta a maboyar ’yan bindigar sun tsananta matsalar lafiyarsa.
An kuma ce duk da ƙoƙarin da Ali Tukur Gantsa ya yi na ƙarfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, lafiyar Anas ta ci gaba da taɓarɓarewa har ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun fara ɓoye rasuwarsa kafin daga bisani ɗaya daga cikinsu ya bayyana cewa tsohon ɗan majalisar ya mutu.
Wata majiya ta cikin gida ta bayyana cewa ɗan marigayin tare da direbansa ne suka kai kuɗin fansar ga masu garkuwar. Bayan karɓar kuɗin, an sako Gantsa tare da nuna wa ɗan marigayin gawar mahaifinsa.
Har zuwa lokacin haza wannan rahoto, reshen jam’iyyar ADC na jihar Jigawa bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da lamarin.
Sai dai an samu bayanan cewa ana kan hanyarsu da gawar marigayin zuwa Kano domin shirye-shiryen jana’izarsa.
Lamarin ya sake ƙara nuna yadda matsalar rashin tsaro da satar mutane ke ci gaba da ƙamari a Nijeriya duk da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin daƙile ayyukan ’yan bindiga. Iyalan mutane da dama na ci gaba da rasa dukiyoyinsu wajen tara kuɗin fansa, yayin da wasu ke rasa ’yan uwansu ko bayan biyan kuɗin.
