An gudanar da taron goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kano na ADC, Malam Ibrahim Khalil

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kungiyoyin magoya bayan Malam Ibrahim Khalil sun gudanar da gagarumin taron nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Malam Ibrahim Khalil, inda dumbin jama’a daga sassa daban-daban suka halarta.

Taron ya samu halartar farfesoshi, malaman addinin Musulunci, wakilan Kiristoci, mata, matasa da sauran magoya bayan jam’iyyar ADC, wadanda suka hallara domin nuna goyon baya ga takarar Malam Ibrahim Khalil gabanin zaben da ke tafe.

Masu jawabi daban-daban sun bayyana damuwa kan halin matsin rayuwa da matsalolin tattalin arziki da siyasa da al’umma ke fuskanta a jihar Kano da Nijeriya baki daya. Sun bayyana cewa jam’iyyar ADC na da manufofi da za su iya kawo sauyi mai anfani da kuma inganta rayuwar talakawa.

Sun kuma buƙaci jama’a da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC) tare da fitowa domin kada ƙuri’unsu ga Jam’iyyar ADC a lokacin zaɓe.

Da yake jawabi a wajen taron, dan takarar gwamnan Kano na ADC, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa shigarsa siyasa ba domin neman amfani na kai ba ne, illa domin kare muradun talakawa da kuma taimakawa wajen magance matsalolin da suke addabar al’umma.

Ya ce da a ce jama’a na rayuwa cikin walwala da kwanciyar hankali ba tare da wahala da rashin adalci ba, da bai shiga siyasa ba. Sai dai saboda halin da al’umma ke ciki, dole ne a ci gaba da fafutukar samar da adalci, daidaito da kyakkyawan shugabanci.

Malam Ibrahim Khalil ya jaddada cewa idan aka ba shi dama zai mayar da hankali wajen bunƙasa ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da shugabanci nagari wanda zai kula da buƙatun kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna bambanci ba.

Shi ma wani wakili daga bangaren Kiristoci da ya yi jawabi a wajen taron ya bayyana cewa suna da yakinin Malam Ibrahim Khalil zai samar da shugabanci na gari da zai hada kan al’umma tare da kawo cigaba a jihar Kano.

Ya ce shi da sauran Kiristocin jihar Kano za su mara wa dan takarar baya tare da amfani da kuri’unsu wajen tabbatar da nasararsa a zabe mai zuwa.

An kammala taron cikin lumana tare da kira ga hadin kai, zaman lafiya da kuma shiga harkokin siyasa cikin fahimta da mutunta juna domin gina Kano da Nijeriya mai inganci ga kowa.

By ukarofi