Daga DAUDA USMAN a Legas
An shawarci al’ummar Musulmi mazauna jihar Legas da ma Nijeriya baki ɗaya da su ƙara himma wajen gyara da kula da maƙabartu, kasancewar su ne gidajen gaskiya na kowa bayan mutuwa.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Malam Ibrahim Mai Gemu, ɗan asalin ƙaramar hukumar Rogo ta jihar Kano, wanda ke zaune a unguwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, kuma shugaban kwamitin kula da gyaran maƙabartun yankin.
Malam Ibrahim Mai Gemu ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar aikin cikon ƙasa a maƙabartun Mile 12 a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce akwai buƙatar Musulmi su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan alheri, domin hakan shi ne mafita ga rayuwar duniya da lahira baki ɗaya.
Malamin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da attajiran ƙasar nan da su riƙa amfani da dukiyoyinsu wajen ayyukan alheri da taimaka wa mabukata a lokacin da suke cikin buƙata.
Hakazalika, ya bayyana aikin gyaran maƙabartun Mile 12 a matsayin wata babbar dama ta saka hannun jari a “kamfanin Allah”, yana mai jaddada cewa ladan irin wannan aiki yana da girma a wajen Allah.
Malam Ibrahim Mai Gemu ya ce akwai maƙabartu guda biyu da ake amfani da su wajen binne mamatan Musulmi a yankin Mile 12, amma ɗaya daga cikinsu ta cika sakamakon yawan jana’izar da ake yi daga sassa daban-daban na jihar Legas.
Ya bayyana cewa an taɓa yin ciko a maƙabartar sau uku a baya, amma duk da haka ta sake cikewa, lamarin da ya sa kwamitin ya yanke shawarar neman taimako daga hannun al’ummar Musulmi domin sake yi mata ciko ta koma yadda take a da.
Ya ƙara da cewa, ɗayar makabartar da ake amfani da ita ma na fuskantar barazanar ruwa, wanda hakan ke kawo matsala wajen binne gawa.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa tun bayan fara aikin cikon ƙasa a makabartun kimanin shekara guda da ta gabata, an zuba tifar ƙasa sama da 150 a wuraren.
Saboda haka ne ya sake roƙon taimako daga hannun Musulmi, ko da kuɗi ne ko kuma tifar ƙasa, yana mai cewa duk irin gudunmawar da mutum zai iya bayarwa za ta taimaka matuƙa wajen ci gaba da aikin.
A ƙarshe, Malam Ibrahim Mai Gemu ya nuna fatan cewa masu kuɗi da sauran al’ummar Musulmi za su ci gaba da ba da gudunmawa domin tallafa wa wannan aiki na alheri.
