Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ahmed Sanusi, ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar Matan Jami’an ‘Yan Sanda ta Nijeriya (POWA) reshen Abuja, ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Hajiya Maimuna Sanusi, a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Garki a Abuja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Talata.
A yayin ziyarar, shugabar POWA, Hajiya Maimuna Sanusi, ta yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan bisa amincewa da ziyarar tare da jinjinawa salon jagorancinsa da ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da tsaro da lafiyar mazauna Babban Birnin Tarayya.
Ta kuma sake jaddada aniyar ƙungiyar wajen ci gaba da tallafa wa jami’an ’yan sanda da iyalansu, tare da bunƙasa walwala da haɗin kai tsakanin iyalan jami’an tsaro a faɗin rundunar.
Hajiya Sanusi ta bayyana cewa ƙungiyar na yaba wa sadaukarwa da jajircewar jami’an ’yan sanda wajen gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tana mai tabbatar musu da cewa POWA za ta ci gaba da ba su goyon baya da ƙarfafawa.
Ta ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da neman shawarwari da haɗin kan shugabannin rundunar domin cimma manufofinta da kuma inganta jin daɗin iyalan jami’an ’yan sanda.
Da yake nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, CP Ahmed Sanusi, ya gode wa tawagar bisa ziyarar tare da bayyana muhimmiyar rawar da POWA ke takawa wajen tallafa wa jami’an ‘yan sanda da kuma ƙarfafa kyawawan ɗabi’u da zaman lafiya a cikin iyalan jami’an tsaro.
Ya tabbatar wa ƙungiyar da cikakken goyon bayan rundunar ga shirye-shiryenta da ayyukanta da ke da nufin inganta walwala da jin daɗin iyalan jami’an ’yan sanda.
Kwamishinan ya kuma ƙarfafa wa mambobin POWA gwiwa da su ci gaba da bai wa mazajensu goyon baya, yana mai cewa kwanciyar hankali da ƙarfafawar da jami’ai ke samu daga iyalansu na taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan tsaro da hidimar jama’a.
An kammala ziyarar ne da saƙonnin fatan alheri tare da sake tabbatar da haɗin kai tsakanin rundunar da ƙungiyar wajen bunƙasa walwalar jami’an ’yan sanda da kuma tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Abuja.
