Nijeriya za ta iya zama cibiyar samar da magunguna a Afirka — Shugaban NAIP

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar Masana Haɗa Magunguna ta Masana’antu ta Nijeriya (NAIP), Pharm. (Sir) Bankole Ezebuilo, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ƙarfafa tallafi ga masana’antun haɗa magunguna na cikin gida domin rage dogaro da shigo da magunguna daga ƙasashen waje tare da mayar da Nijeriya cibiyar samar da magunguna a nahiyar Afirka.

Ezebuilo ya bayyana hakan ne yayin taron ƙasa karo na 29 na shekara-shekara da horaswar ƙungiyar NAIP da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Da yake jawabi a taron mai taken: “Haɗin Gwiwa da ƙirƙire-ƙirƙire Domin Gina Mafita Ta Cikin Gida Don Makomar Masana’antar Magunguna ta Nijeriya,” shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya miƙa tsaron lafiyar al’ummarta ga wasu ƙasashe.

Ya bayyana wa masu ruwa da tsaki a ɓangaren magunguna, hukumomin sa ido, masana’antun haɗa magunguna, masu tsara manufofi da ƙwararrun ma’aikatan lafiya cewa a halin yanzu Nijeriya na shigo da sama da kashi 70 cikin ɗari na magungunanta daga ƙasashen waje, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga tsarin kiwon lafiya da tattalin arzikin ƙasa.

“Akwai haɗari babba idan ƙasa ba za ta iya samar da magungunanta da kanta ba. Idan muka yi abin da ya dace, za mu bunƙasa wannan masana’anta, mu samar da ayyukan yi, mu rage dogaro da ƙasashen waje tare da samar da ingantaccen tsarin lafiya a gida,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “ƙasar da ba za ta iya samar da magungunanta ba, tana yin sulhu ne da lafiyar al’ummarta, kuma ba lokacin yin sulhu ba ne idan rayuka ke cikin haɗari.”

Ezebuilo ya bayyana cewa Nijeriya na tsaka mai wuya tsakanin ci gaba da dogaro da shigo da magunguna daga ƙasashen waje ko kuma rungumar cikakken ikon sarrafa harkokin magunguna ta hanyar ƙarfafa samarwa a cikin gida.

A cewarsa, domin sauya wannan yanayi, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren masana’antar hada magunguna tare da aiwatar da manufofin da za su mayar da Nijeriya cibiyar samar da magunguna ta Afirka baki ɗaya.

Ya tabbatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa ƙungiyar NAIP ta horar da mambobinta kuma tana shirye tsaf domin yin aiki tare da gwamnati wajen jagorantar juyin juya halin masana’antar magunguna a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar ya kuma ce ɗorewar tsarin kiwon lafiya ba abu ne da za a iya shigo da shi daga waje ba, sai an gina shi da niyya ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati, masana’antu, jami’o’i, hukumomin sa ido da ƙungiyoyin ci gaba.

Ezebuilo ya yi gargaɗin cewa duk ƙasar da ba za ta iya samar da magungunanta da kanta ba za ta kasance cikin haɗari yayin ɓarkewar annoba ko rikicin lafiya na duniya.

Ya bayyana cewa duk da Nijeriya na samar da wasu magunguna a cikin gida, yawancin sinadaran haɗa magunguna masu muhimmanci (APIs) har yanzu ana shigo da su daga ƙasashen waje.

A cewarsa, cimma cikakken ikon samar da magunguna a gida zai taimaka wajen tabbatar da wadatar magunguna, inganta kula da inganci, samar da ayyukan yi, rage kashe kuɗaɗen musayar waje tare da mayar da Nijeriya cibiyar masana’antu a yankin.

Ya kuma ƙalubalanci masana da masu ruwa da tsaki a harkar magunguna da su daina dogaro da ra’ayoyi daga ƙasashen waje kawai, yana mai cewa: “Domin gina mafita ta cikin gida, dole ne mu daina shigo da magunguna kaɗai, har ma da tunani. Hanya mafi kyau ta hasashen makoma ita ce mu ƙirƙire ta da kanmu.”

A yayin taron, Ezebuilo ya ƙaddamar da gyaran cibiyoyin lafiya da darajarsu ta kai miliyoyin naira a Fadar Sarkin Ilorin domin ƙarfafa kiwon lafiya a matakin ƙasa.

By ukarofi