
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta wallafa sunayen masu neman kujeru a Majalisar Wakilai da ta hana takara a zaɓen fidda gwani a wasu jihohi da suka haɗa da Ondo, Bauchi, Ebonyi, Kogi da kuma Ribas yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.
An sako jaddawalin sunayen nasu ne a ranar Asabar a wata takarda da Sakataren yaɗa labarai na ƙasa Felix Morka ya fitar bayan kammala tantance ‘yan takarar da ke neman tikitin tsaya wa takara a jam’iyyar.
A cewar sanarwar, kwamitin tantancewar ya yi nazari akan ‘yan takarar ne bisa la’akari da sharuɗɗan APC da hanyoyin da ake bi wajen tantance waɗanda za su shiga sahun masu fafatawa a kujerar daban-daban na mazaɓun tarayya.
Ga jaddawalin kamar yadda jam’iyyar ta fitar:
Ondo: Hon. Adefisoye Tajudeen, Olusegun Victor Ategbole, Seun Oluwashina Ajongbolo, Rt. Hon. Arowole Ayodeji Samuel, Morufu Tosin Ibrahim, Oseni Oyeniyi da kuma Olaleye John Adedipe.
Bauchi: Dakta Bashir Ibrahim Bello
Ebonyi: Hon. Idu Igariwe
Kogi: Sanni Salau Ogembe
Ribas: Air Commodore John Azubuike Opara, Uni (RTD), Hon. Anderson Allison Igbiki, Awaji Imombek D. Abirite da kuma Hon. Boma Goodhead.
