Ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazaɓar Mani/Bindawa da ke jihar Katsina, Ahmed Saleh Junior, ya zargi gwamnatin jihar da wasu shugabannin jam’iyyar APC da hana shi damar shiga zaɓen fidda gwani da aka yi na mazabar Mani/Bindawa ta hanyar tsare shi har sai da aka kammala zabe aka sake shi Wanda ya bayyana haka a matsayin rashin adalci.
Saleh Junior ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a garin Mani inda ya ce jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama shi tare da tsare shi har sai bayan an kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazaɓar.
Ya bayyana cewa ya bi dukkan matakan da jam’iyyar ta APC ta shimfiɗa domin neman tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya domin wakiltar alummar sa.
A cewar sa ya sayi fom ɗin tsayawa takara da na nuna sha’awa, sannan ya halarci tantancewa inda aka tabbatar da cancantarsa.
Ya bayyana cewa shugabannin APC na jihar Katsina tare da gwamnatin jihar sun amince da amfani da tsarin sasanci wajen zakulo ‘yantakarar jam’iyyar.
“An kafa kwamitin sasanci karkashin jagorancin Arc. Ahmed Dangiwa, inda daga bisani masu ruwa da tsaki daga mazaɓar Mani/Bindawa gaba Daya suka amince da shi a matsayin ɗantakarar sasanci na APC,”Inji juniya.
“Gwamnatin Katsina da jam’iyya sun taya ni murna a hukumanc har ma aka wallafa sunana a kundin APC na jihar Katsina,” in ji shi.
Sai dai ya ce bayan awanni 24 da ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sasancin farko, wasu daga cikin masu neman takarar sun garzaya wajen gwamnan jihar suna korafin cewa ba a gudanar da tsarin sasancin da yardarsu ba. A cewarsa, hakan ya sa gwamnan jihar ya umurci kwamitin da ya sake gudanar da wani sabon sasanci da zai haɗa dukkan masu neman takarar guda biyar.
Ahmed Saleh Junior ya ce yayin sabon sasancin an gudanar da kaɗa ƙuri’a kaitsaye, inda ya samu ƙuri’u 25 cikin 27, yayin da sauran ‘yantakarar suka samu sifili.
“An ayyana ni a matsayin wanda ya yi nasara karo na biyu, mutane suka yi murna. Amma abin mamaki, daga baya aka bai wa Jamila Maigoyo tikitin takarar duk da cewa ba ta samu ko ƙuri’a ɗaya ba,” in ji shi.
Juniya ya ce wannan rashin adalci da akai Masa tamkar fashi da makami ne akayi masu.
Ya ce duk da haka ba zai fice daga jam’iyar APC ba Kuma zai bada cikakken goyon baya da gudunmuwa na ganin Bola Tinubu ya ci zaɓe a yankin.
Sai dai ya zargi jami’an DSS da kama shi a ranar da aka tsara gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye wato a yau Juma’a.
“An kama ni aka tsare ni har sai da aka kammala zaɓen fidda gwani sannan aka sake ni. Har zuwa yanzu babu wanda ya gaya min dalilin kama ni,” yana mai zargin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani ba a mazabar Mani/Bindawa.
A cewarsa, an tattaro wasu mutane daga sassa daban-daban na mazabar a wuri guda sannan aka sanar da wanda gwamnati ke so a matsayin wanda ya yi nasara.
“Ba zai yiwu a ce an gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya ba alhali ɗaya daga cikin manyan masu neman takarar ba ya wajen saboda an kama shi,” in ji shi.
Ahmed Saleh Junior ya bayyana matakin da aka ɗauka a kansa a matsayin abin takaici, yana mai cewa ya kasance mai biyayya ga gwamnati da jam’iyyar APC tsawon lokaci, yana mai tambayar cewa me ya tsare wa gwamnati ko jam’iyyar da har za a yi masa haka?
Ya ce ya bar komai ga Allah da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC. Saleh Junior ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a garin Mani inda ya ce jami’an Hukumar tsaro ta DSS sun kama shi tare da tsare shi har sai bayan an kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazaɓar.
Ya bayyana cewa ya bi dukkan matakan da jam’iyyar ta APC ta shimfiɗa domin neman tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya domin wakiltar alummar sa.
A cewar sa ya sayi fom ɗin tsayawa takara da na nuna sha’awa, sannan ya halarci tantancewa inda aka tabbatar da cancantarsa.
Ya bayyana cewa shugabannin APC na jihar Katsina tare da gwamnatin jihar sun amince da amfani da tsarin sasanci wajen zaƙulo ‘yan takarar jam’iyyar.
“An kafa kwamitin sasanci ƙarƙashin jagorancin Arc. Ahmed Dangiwa, inda daga bisani masu ruwa da tsaki daga mazaɓar Mani/Bindawa gaba ɗaya suka amince da shi a matsayin ɗan takarar sasanci na APC,”Inji juniya.
“Gwamnatin Katsina da Jam’iyya sun taya ni murna a hukumance har ma aka wallafa sunana a kundin APC na jihar Katsina,” in ji shi.
Sai dai ya ce bayan awanni 24 da ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sasancin farko, wasu daga cikin masu neman takarar sun garzaya wajen gwamnan jihar suna ƙorafin cewa ba a gudanar da tsarin sasancin da yardarsu ba. A cewarsa, hakan ya sa gwamnan jihar ya umurci kwamitin da ya sake gudanar da wani sabon sasanci da zai haɗa dukkan masu neman takarar guda biyar.
Ahmed Saleh Junior ya ce yayin sabon sasancin an gudanar da kaɗa ƙuri’a kai tsaye, inda ya samu ƙuri’u 25 cikin 27, yayin da sauran ‘yantakarar suka samu sifili.
“An ayyana ni a matsayin wanda ya yi nasara karo na biyu, mutane suka yi murna. Amma abin mamaki, daga baya aka bai wa Jamila Maigoyo tikitin takarar duk da cewa ba ta samu ko ƙuri’a ɗaya ba,” in ji shi.
Juniya ya ce wannan rashin adalci da akai masa tamkar fashi da makami ne akayi masu.
Ya ce duk da haka ba zai fice daga jam’iyar APC ba Kuma zai bada cikakken goyon baya da gudunmuwa na ganin Bola Tinubu ya ci zaɓe a yankin.
