Attajiri ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen fidda gwani na APC a Balanga/Billiri

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai neman wakiltar mazaɓar Balanga/Billiri a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Alfred John Attajiri, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani da aka bayyana, yana mai zargin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓe ba a mazaɓar kafin sanar da sakamakon.

Attajiri ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce sanar da sakamakon zaɓen da bai gudana ba barazana ce ga dimokuraɗiyya da kuma mutuncin jam’iyyar APC.

Ya zargi tsohon kwamishina a Jihar Gombe, Hon. Mohammed Sa’idu Yila Fawu, da sanar da sakamakon wani zaɓe da, a cewarsa, bai taɓa gudana ba a ƙananan hukumomin Balanga da Billiri.

A cewarsa, bayanan da ya samu daga mambobin jam’iyyar, tare da hotuna, bidiyo da shaidu daga wurare daban-daban, sun nuna cewa ba a gudanar da kaɗa ƙuri’a ba a sassa da dama na mazaɓar.

“Abin takaici ne a sanar da sakamakon zaɓen da bai gudana ba. Wannan lamari ya tauye haƙƙin dimokuraɗiyyar mambobin jam’iyya tare da kawo barazana ga martabar APC,” in ji shi.

Ya bayyana cewa irin wannan mataki na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓukan cikin gida na jam’iyyar, yana mai kira ga shugabannin APC na ƙasa da su shiga lamarin domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Attajiri ya kuma roƙi Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe, da su sa baki wajen binciken lamarin tare da tabbatar da an yi wa kowa adalci.

Sai dai duk da korafin da yake yi, Attajiri ya buƙaci magoya bayansa da al’ummar mazaɓar da su kasance masu bin doka da oda tare da kaucewa duk wani tashin hankali.

“Gwagwarmayarmu ta tabbatar da adalci ce, ba rikici ba. Muna da yaƙinin cewa gaskiya za ta yi nasara,” in ji shi

By ukarofi