Sarkin Musulmi ya sanar da 27 ga Mayu a matsayin ranar Babbar Sallar 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar kuma Shugaban Majalisar Ƙolin Shari’a ta Ƙasa (NSCIA), ya ayyana ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 a matsayin ranar 1 ga Dhul Hjjah, 1447.

Shugaban kwamitin mashawarta akan harkokin addinin Musulunci kuma Wazirin Sakkwato, Sambo Wali Junaidu ya sanar da haka a yau Lahadi acikin wata takarda.

A cewar saƙon takardar, an sanar da batun ne bayan tabbatar da ganin jaririn watan, wanda ke nuna an shiga watan ƙarshe a kalandar Musulunci.

Wannan wata na ɗaya daga cikin watanni masu alfarma a Musulunci saboda falalarsa domin a ciki ake yin ibadun Babbar Sallah, wato Eid al-Adha da kuma aikin hajji.

Majalisar Sarkin ta kuma yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa alaƙarsu da Mahaliccinsu ta hanyar yin ibadu da addu’o’in nema wa ƙasa zaman lafiya, haɗin kai da kuma ci-gaba mai ɗorewa.

By Babaji