Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC ta ƙasa ta shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar majalisar tarayya a gobe Litinin.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen da jam’iyyar ta APC ta ƙasa ta turo a Jihar Dr. Auwal Abdullahi Aliyu ya bayyana hakan a zantawar SA da manema labarai a Gusau yau Litinin.
A cewar sa, kwamitin su zai tabbatar da an gudanar da zaɓen fidda gwanin cikin adalci da nasara.
Dr. Abdullahi ya ƙara da cewar, kwamitin sa ya samu labarin wasu sun ayyana kansu a matsayin kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwanin a Jihar Zamfara, yana mai nuni da cewar, hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa ba ta da masaniya, kuma kwamitin sa ne halartacce daga jam’iyyar ta ƙasa.
“Mu samu labarin wasu Suna ikirarin cewa sune kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na yan takarar majalisar tarayya da zai gudana a gobe a Jihar Zamfara, waɗannan mutane ba halatattu bane, mune aka turo daga jam’iyyar APC ta ƙasa mu gudanar da zaɓen”. Yace
Ya yi kira ga yan siyasa a Jihar musamman yan jam’iyyar APC da su bada goyon bayan da ya dace don kammala zaɓen fidda gwanin cikin kwanciyar hankali da Nasara
