
Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya samu amincewar kwamitin tantance ‘yan takarar jam’iyyar APC domin shiga zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya a zaɓen 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa sunan Yahaya Bello ya fito cikin jerin ‘yan takara 17 da APC ta tantance daga yankunan sanatoci uku na jihar domin fafatawa a zaɓen fidda gwani da za a gudanar ranar Litinin.
A kwanakin baya dai an yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan na iya fuskantar cikas wajen samun damar shiga takarar, sai dai fitowar sunansa cikin jerin waɗanda aka tantance ya kawo ƙarshen jita-jitar.
Yahaya Bello zai fafata ne da Momoh Yusuf Obaro da Ibrahim Yakubu Adoke domin neman tikitin APC na Sanatan Kogi Central.
A yankin Kogi ta Yamma kuma, Sanata Sunday Karimi ya zama ɗan takarar sasanci bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo a gidan gwamnati da ke Lokoja.
Kodayake akwai wasu ‘yan takara shida da aka tantance ciki har da tsohon Sanata Smart Adeyemi da Aro Bamidele, masu bibiyar siyasa na ganin Karimi na da ƙarfi saboda tsarin sulhun da aka cimma.
Haka kuma a Kogi ta Gabas, APC ta tantance ‘yan takara bakwai da suka haɗa da Sanata Isah Echocho, Joseph Ameh da Murtala Ajaka domin neman tikitin sanatoci.
A ɓangaren jam’iyyar PDP kuwa, an samu fitar da ‘yan takarar majalisar wakilai ta hanyar sasanci a wasu mazaɓu daban-daban na jihar.
Tsohon ɗan majalisa, Abdulrahman Badamasuiy ya zama ɗan takarar PDP na mazabar Okehi/Adavi, yayin da Mohammed A. Etudaiye da Lawal Idrisu suka samu tikiti a wasu mazaɓu ta hanyar yarjejeniya.
