Daga JOHN DOGO WADA a Lafiya
Alhaji Abubakar Giza ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa ne a inuwar jami’ar Zenith Labor Party (ZLP). A tattaunawar nan na musamman da Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Nasarawa, JOHN DOGO WADA, ya yi da shi ya bayyana dalilin fitowarsa takarar da ire-iren ayyukan cigaban da zai gudanar in ya yi nasara da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:
MANHAJA: Me kake niyyar yi wa Jihar Nasarawa idan ka yi nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar?
ALHAJI ABUBAKAR: Ba burina ba ne na nemi zama gwamna da kaina. Ina Amurka ne a lokacin da mutanena a gida Nijeriya suka zo suka ce in fito takarar gwamnan. Dalilin da suka zo shi ne wannan ƙauna da nake da ita ga Jihar Nasarawa tun 1991.Ni ne na rubuta takardar shawara don a ƙirƙiri Jihar Nasarawa. Na fara a zamanin Babangida, mun je ko’ina amma wasu a kwamitin suka hana saboda ba sa son a taɓa Filato. Sa’an nan a zamanin Abacha na sake farawa.
Na sake rubuta takarda na yi yawo har sai da aka ƙirƙiri jihar. Bayan haka na shiga ayyukan gwamnatin tarayya kuma duk abin da nake yi shi ne in taimaki mutane. Tun 2011 sama da mutane 500 daga jihar nan ta Nasarawa na samar musu aiki ta hannuna. Ban nema komai ba. Abin da nake so kawai shi ne iyalai su tsaya da ƙafunsu. Lokacin da mutane suka zo suka ce “ka dawo gida ka tsaya takar gwamna,” na gaya musu ban san yadda ake yin ƙarya ba. Amma suka ce sun ga abin da na yi kuma suna son wannan ƙwazon da halin da nake da shi ga jihar. Daganan sai na fara yin yawo ko’ina a jihar nan na nemi shawarwari kuma abin da na ji shi ne: “mu ne muka ce su je su kawo ka.”
Shi ya sa nake nan. Abin da ke motsa ni shi ne in bunkasa Jihar Nasarawa da mutanen ta. Kaga Jihar Nasarawa tana da arziƙi amma ba mu amfani da ita yadda ya dace. Mayar da hankali na zai kasance a kan abubuwa masu amfani da za su kawo aiki da kuɗin shiga:l Wutar Lantarki daga Farin Ruwa, Wamba. Idan muka bunƙasa Farin Ruwa yadda ya kamata zai iya ba Abuja da Nasarawa wuta. Ba tare da wuta ba kamar yadda ka sani babu masana’anta da za ta tsaya.
Da wannan wuta zamu iya kawo masana’antu 3, 4, 5. Kowace masana’anta za ta iya ɗaukar aƙalla mutane 10,000. Wannan zai kawo aiki ga matasanmu da kuɗi ga jihar da masu saka jari. Je kowace gida a Nasarawa za ka ga matasa 5, 6, 10 da suka kammala karatu suna zaune ba su da abin yi. Mata suna zuwa gona suna wahala don su horar da ‘ya’yansu amma idan suka gama ‘ya’yan sukan dawo gida a cigaba da ciyar da su. Wannan ba abin yarda ba ne. Manufata shi ne in canza hakan ta hanyar samar da yanayin da mutane za su sami aiki ta hanyar masana’antu da noma da horar da mutanenmu. Lokacin da nake Darakta a Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ni ne na ƙirƙiri tsarin PAYE da Jihar Nasarawa ke amfana da shi yanzu. Jiha na karɓar ɗaruruwan miliyoyi cikin kowane wata. Na yi hakan ne saboda ƙaunar da nake da ita ga jihar ba saboda ina neman mulki ba.
Me za ka ce game da ra’ayin wasu ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki cewa Jihar Nasarawa na buƙatar daidaito ta hanyar zoning?
Mutane suna ta maganar zoning amma a gare ni uzuri ne na rashin ƙwarewa. Kaga kamar yadda ka sani yankin Kudancin Sanata na jihar nan sun yi shekaru 12 suma mulki. Abin da ke da muhimmanci shi ne wa ke da ƙwarewa da mutunci don ya bunƙasa jihar? Ko dai Akwanga da Lafia ne kawai ke son riƙe zoning to su riƙe. Bari mutanen Nasarawa baki ɗaya su zaɓi wanda suke ganin zai bunƙasa jihar. Muna buƙatar ƙwarewa da farko. Mutane marasa ƙwarewa suna shigowa su tattara dukiyar jihar su tafi su bar jama’a da wahala.
Za ka fafata da manyan ‘yan takarar kujerar gwamnan daga APC da PDP da sauran jam’iyyu. Ka na ganin zaka iya ka da su?
Ban damu da APC ko PDP ko wata jam’iyya ba. Wannan fitowa na takarar ba game da ni ba ne kamar yadda na bayyana maka dafarko amma game da mutanen Jihar Nasarawa ne. Kuma daga abin da na gani mutane sun shirya su zaɓi wanda zai yi gaskiya ya zama mai gaskiya da bayyana kuma zai bunƙasa jihar. Ban taɓa cewa ina so in zama gwamna ba. Amma koyaushe ina cewa ina so in taimaki mutane. Shi ne abin da nake kawowa yanzu cikin wannan tserin.
Mun gode sosai.
Ni ma na gode.
