A kiyaye martabar aure da mutuncin iyalinmu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mai karatu, nasan ba za ka kasa jin labarin nan da ya karaɗe kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta ba, wanda aka ce wasu mutane bakwai a garin Azare da ke cikin ƙaramar Hukumar Karagum suna musanyar matansu na aure a tsakanin su.

Mutumin da ya ɓullo da wannan sabon tsarin ya ce a mafarki ya gani ana umartarsa da su fara musanyar matansu a tsakaninsa da abokanensa su bakwai, waɗanda suka yi imani da wannan aƙida mai suna “Huddadu”. Binciken rundunar Hisba ta garin Azare ya gano cewa, an kwana biyu ana wannan musanyen mata tsakanin waɗannan mazaje, kafin bayyanar lamarin a bainar jama’a. 

Idan ta tabbata wannan labarin da gaske ne, ko kuma yadda aka ba da labarin tabbas haka ya faru to, lallai za mu ce tir da masu aikata irin wannan ƙazamin aiki. Kodayake, na ga wasu mazauna garin na Azare suna ƙoƙarin bayyana cewa abin da ake yaɗawa ba haka ba ne.

To, ko ma dai yaya abin ya faru sunan garin Azare ya shiga tarihin duniya kan wannan ƙazamin aiki. Duk da kasancewar gari ne na bayin Allah masu kiyaye addini da riƙo da tarbiyyar Musulunci. Gari ne na ilimi, noma da kiwo, kuma garin da ya samar da fitattun ’yan boko da malaman addini. Amma kamar yadda ake samu a ko’ina, akwai mutane salihai, akwai kuma baragurbi waɗanda son zuciyarsu ne kawai a gabansu.

Sai dai maƙasudin wannan rubutu nawa na yau shi ne jan hankali ga magidanta da su riƙa kiyaye martabar iyalinsu. Watsi da haƙƙoƙin iyali da kasa sauke nauyin da Allah Ya ɗora mana na kula da tarbiyyar su da addininsu, babban haɗari ne ga wannan al’umma. Ballantana, wofintar da mutuncinsu da musanyensu da wasu mazajen da ba muharraman su ba, da sunan biyayya ga wani tsari da ya saɓa da mutuntakar ɗan adam da koyarwar addini.

A fahimta ta, jahilci da son zuciya ne yake sa mutane aikata irin haka. Abin takaici ne ka ji wasu magidanta suna kwaikwayon abubuwan da suke gani a finafinan batsa wanda Turawan Yamma suke shiryawa. A ce ɗan Musulmi ne zai gayyato wani namiji ya yi amfani da matarsa a kan idonsa, ko kuma su yi amfani da ita a lokaci guda. A wani lokacin kuma matarsa ce za ta gayyato wata mace daban ɗakin aurenta, sai mijinta ya yi amfani da su a tare. Ana kuma samun maza biyu ko uku da za su haɗu a ɗaki ɗaya kowanne da matarsa ko budurwarsa, sai mazan su riƙa musanyen matan a tsakanin su, kowanne na amfani da wacce yake so.

Wannan abin fa ba tatsuniya ba ce, zahiri ne yana faruwa ba a finafinai ba, a tsakanin al’ummar musulmi. Duk da kasancewar abubuwa ne da ake gudanarwa a ɓoye bisa amincewar juna, amma lokaci-lokaci asiri kan tonu ko kuma a samu wani saɓani har labari ya bayyana. Kar ku yi mamakin jin cewa wannan ɗanyen aiki ba a birni kawai yake faruwa ba, ya ma fi faruwa a ƙauyuka, inda jahilci da wauta suka yi katutu.

Na daɗe ina takaici kan wani labari da aka bani na wani mutum da ya yi hayar abokinsa don ya kwanta da amaryarsa, wacce aka ce ya kasa buɗe ta a daren farko. Bayan su yi jinga da abokin akan zai kwanta da matarsa ya buɗe masa ita a kwana uku sai ga shi matar ta haɗa baki da abokin nasa aka ce wa angon ƙofa ba ta buɗe ba, har tsawon wasu kwanaki. Daga bisani dai a ofishin ’yan sanda aka yanke hukunci.

Ire-iren wannan kwamacalar tana nan da yawa, sai iya abin da mutum ya ji, ko ya gani. Duk da nasihohi da malamai ke yi a masallatai da wuraren ibada, har yanzu jahilci na cigaba da jefa magidanta da dama cikin halaka. Wasu da dama sun ɗauki batun aure kamar wasa, ba sa kiyaye martabar aurensu da mutuncin iyalinsu, suna yaudarar matan da maganganu na jahilci da soki-burutsu, don su aikata son zuciyarsu.

Lallai ne iyaye su riƙa kula da mazajen da za su aurar wa da ’ya’yansu mata. Su yi bincike sosai kamar yadda addini ya gindaya, a tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwarsa, ingancin aƙidarsa, da iliminsa na addini. Hakan shi zai bai wa uba kwanciyar hankali da natsuwa, kan wanda yake riƙe masa da ’yarsa. Amma idan iyaye suka cigaba da nuna sun matsu su aurar da ’ya’yansu ga duk wanda ya zo neman aurenta babu bincike to, babu shakka abin kunya da takaici zai ci gaba da bibiyar mu.

Mu riƙa bincike da bibiyar yadda ’ya’yanmu mata suke zaune a gidan mazajensu, kwanciyar hankalinsu, da kula da addininsu da haƙƙoƙin su. Mutumin tabbatar ba a cutar da su ba, ba a tauye musu haƙƙi ba, kuma ba a ɗora su a kan wannan mummunar hanya ba. Haƙƙin mu ne mu kula da amanar iyalinmu da Allah Ya damƙa ta a hannun mu, mu daina sakaci kan sauke nauyin da ke kanmu. Ta haka ne kawai za mu iya tsaftace al’ummarmu daga munanan aƙidu da salon rayuwa marar kyau.

By ukarofi