Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Haƙiƙa ikirarin wai ASABIYYA ta taimaki Manzon Allah mai tsira da aminci, kawai dattin kiyayyace ga addinin tauhidi. Wai da a ka tasamma Manzon Allah SAW da barazanar kisa sai a ka mika aikin ga Banu Hashim su kuma su ka ki cika aiki don kare ƙabila! Duk wata hanya ko ta rubutu ne ko furtawa dab aka da ta taba darajar Manzon Allah to ba shakka akwai hatsari mai girma a ciki don ƙetare haddi ne da neman tsokana.
Marubucin ‘yan bazata ya kawo tarihi na cin zarafi ga Manzon Allah inda ya yI iƙirarin wai da a ka tasamma MANZO SAW da nufin kisa sai a ka miƙa aikin ga Hashimawa inda su kuma su ka ki cika aikin. Marubucin wanda a baya ya zagi Annabi mai tsira da aminci, ya ce hakan ASABIYYA ce wato KABILANCI ya kare Manzon Allah, wai kenan ba don haka ba da Musulunci ba zai wanzu ba! E gaskiya ne ba zai wanzu ba amma a tunanin kafurai da ba su amince da Annabcin Annabi Muhammadu mai tsira da aminci ba.
Shin BANU HASHIM ba zuriyar Larabawa/Kuraishawa ba ce? Shin wadanda ya ke ikirarin sun shirya tuggu ga Manzo ba Kuraishawa ba ne? Me ya kawo kabilanci a nan? Wannan ya nuna cakuɗa bayanai da ganganci ko rashin sani. Hashimawa fa dangi ne da a ke karramawa a nan Makkah don tsarki da tsoron Allah, ba don Larabci ko ƙabilanci ba don sunan na su ya samu asali daga kakan-kakan Manzon Allah Hashim Ibn Abdulmanaf. Babban jigo a dangin wato Baffan Manzon Allah Abu Talib ya zama jagora a lokacin tarihin wannan tuggun kuma ya cigaba da kare Manzon Allah don darajar Manzon Allah mai laƙabi da AMINU AMINTACCE.
Sam Manzon Allah bai nemi kowa ya yI amfani da ƙabilanci ko wata dangantaka don kare shi ba. Manzon Allah fa a ka ce ma ka! Wallahi ka shiga taitayinka. Batun wai da Musulunci bai wanzu ba, na nuna jabbaranci da rashin imani da umurnin Allah wanda ya aiko Manzon Allah ga dukkan halitta kuma wannan saƙo ko umurni ba wani abun halitta kaskantacce mai barci da mutuwa da zai hana shi wanzuwa. Wannan magana babban sabo “Blasphemy” ne ga haƙƙin Manzon Allah SAW.
ƙarara ko mutum ya na so ko ba ya so ASABIYYA haramun ne kuma duk Musulmi ya zama wajibi ya yI watsi da ASABIYYA daga wajen kowaye a ko ina.
Yo in ka na batun Banu Hashin kamar fa ka ce wasu sashe ne a dangogin Hausawa ke son farmaki kan wani jigo a wani dangi kamar misali Gobirawa su nufi Katsinawa da wata manufa. Allah ya sauwake shirme.
Idan ASABIYYA ba ta haramta ba har da misali kan Manzon Allah don zindikanci; mai ya sa a ka yI jihadi kan mutanen na Makkah ciki kuwa har da Hashimawa?
Kwanaki fa wannan marubucin bazata ya kwatanta tsarkin Dutsen Dala da Dakin Ka’aba! Na fito ƙarara na nuna ma sa Dakin Ka’aba na da daraja ta daban don ya na saitin BAITUL MAMUR ne inda mala’iku ke dawafi kamar yadda Musulmi ke yI a nan Makkah.
Lallai a ja wa wannan ɗan bazata Basangwame kunne don ya yi mika ya wuce bargonsa.
Ikon Allah ne ba dabararmu ba yadda a ka wayi duk jama’ar Annabi SAW ke ankara da makircin ‘yan bazata da kan buya a bayan Musulunci don yaki da Musulmi. Gaba da gaba sun gwada wannan arangama amma sun faɗi warwas don haka su ka ɓullo ta katanga da rigar Hausawa.
Hakika ba wanda ‘yan bazata su ka tsana irin Bahaushe don yadda ya tsaya kan biyayya ga Allah SWT da Manzonsa SAW. Wannan ya sa su ke ta ƙoƙarin kore tasirin Musulunci wajen nuna ƙabila ta fi addini.
Logar da ‘yan bazata su ka ɗauko ta yaƙi da Musulunci ba za ta yi mu su sauki ba sai sun murde tarihin gaskiya na Shehu Mujaddadi da cusa wasu tatsuniyoyi da ingiza waɗanda ba su ankare ba su fara kokonton ko ma kuskure su ka yi da su ka riƙi Musulunci sau da kafa.
Wautar ‘yan bazata rashin amincewa da tarihin gaskiya don in sun bi tarihi za su gane miyagu na shekaran jiya ma haka su ka tafi su na cizon yatsa balle a yau da sai ma sun buya a wayar salula sun ƙirƙiri sunayen karya da hotunan AI na bogi kafin fantsama gubarsu. Mai gina ramin mugunta…!
Duk wanda za a karanta ma sa ayar Alkur’ani mai girma da Hadisan Manzon Allah mai tsira da aminci a nusantar da shi haramcin ƙabilanci amma ya yi biris da maganar ko ma ya jefa baƙar magana, ai kun ga akwai lauje cikin nadi. Abun da a ka san Musulmi shi ne sallamawa in a ka ce Allah ya ce Annabi ya ce. A nasu ɓangaren ‘yan bazata kan shashantar da batun da nuna wai lokaci ya wuce da za a yaudare su da addini! Ashe addini yaudara ne dama a wajensu?
Mutanen da addini ya zama yaudara a wajensu ba zai zama wani abun mamaki ba, in ya zama kwangilarsu ta maida hankali ga cin zarafin Shehu Mujaddadi da sauran manyan malaman Musulunci. Idan mutum ba Musulmi ba ne ai don ya faɗa ƙiyayya ta fitar hankali kan addinin ba zai zama wani sabon abu ba sam.
Wannan ya sa mutanen nan sun san ba za su samu nasara ba in su ka fito fili a ka san su ko su waye, shi ya sa su ka zaɓi dinka rigar karya ta Hausawa duk da ‘yan kananan kabilu ne amma kash buyan bai amfane su ba, don ɗabi’unsu na fito na fito da Allah maɗaukakin Sarki sun sa asirinsu ya tonu.
Hanyar da ‘yan bazata su ka bi ta bayan gida ba za ta kai su ga gaci ba. In su na son yaƙi da Musulunci su fito a mutane su yi abunsu kamar yadda magabatansu su ka yi. Inda ba kasa a ke gardamar kokawa. Mun fasa tayar makirai kuma ba dai su yi tasiri a Arewa ba sai dai a tsakanin masu dabi’ar Midibelawa da Biyafarawa.
Iyayen yaudara da makirci, ‘yan bazata da kan raɗawa kansu sunayen Larabawa duk da ba sa ƙaunar Larabawa don sun ce ƙabilarsu ta basaja ta fi Kuraishawa asali, kullum kokarinsu yadda za su shirayawa musulmi gadar zare. Kama daga a na marawa ‘yan ta’adda baya a kan mumbari ko malaman Fulani na ɗaurewa ɓarayi baya da sauran sharri, ba su taba kushe dandamalin da Pasto ke hawa a majami’a ba kuma ba su taɓa magana ko ta bagaye ba idan wani ya yi yunƙurin ɓatanci ga fiyayyen halitta. Kawai logarsu aikin kwangilarsu zagin malaman musulunci da yunƙurin haɗa Musulmi dauki ba daɗi ba da juna a doron canja limami don bambancin ƙabila!. Haba ai a wajen Musulmi ƙabilanci haramun ne har ranar tashin alƙiyama. Su sauya wata dabarar.
Duk sunaye irin Al-waye-waye Hausawy waye me ne ne da sauran tarkace, duk hanyoyi ne na manna kai da Larabci don hakan ya zama hanyar yaudarar waɗanda ba su da dogon nazari. Can cikinsu kuma mafi zakewa kan yi watsi da sunayen da ke alaƙa da Musulunci su na ƙirƙirar wai su CIWAKE, CIDAWA, HATSI YA NUNA da sauransu. Akwai wani farfesa a cikinsu da ke kyamar sunayen Musulunci da buƙatar lallai a rungumi na gargajiya amma shi kansa sunan babban sahabin Manzon Allah ne da shi! Tubka da warwara kenan. Ka ji gasa rago.
Kamar yau ɗin nan Jumma’a za ku ga wasu daga ‘yan bazata na amfani da hotunan manhajar AI wai ga su nan a masallacin Jumma’a. Abun dariya ma ba kalar masallacin a duk duniya ba limami ba saƙon huɗuba ba komai sai hoton AI da wani ya na riƙe da sallaya har ma da tasbaha. ‘Yan bazata sun dauka alamar Musulunci zuwa sallar Jumma’a ko rike carbi ne da darduma ne. In za su yaudari kowa ban da irinmu da kan tantance da tace aya da tsakuwa.
KAMMALAWA
Duk da su na nuna cikinsu akwai mabiya addinin Kirista amma ba sa nuno kansu ranar Lahadi a wani coci tare da sauran mabiya a na addu’a da cire huluna kamar yadda ya ke a tsarin majami’a. Idan akwai wanda ya taba ganin inda wani daga mutanen nan ya nuna kansa a majami’a ya kawo mu gani. Mai ya sa su ke gudun yin hakan? Don ajandar ba ta yaƙi da addinin Kirista ba ne sam.
Shin kun tuna yadda su ka yi wuf su ka shashantar da BAHAUSHE YA MULKI KANSA na fadar Reverend Shu’aibu Bargi sarkin mabiya addinin Kirista na Kano? In har su na da gaskiya mai ya sa ba su ci gaba da nuna yadda a ke zaman faza da yi wa kasa addu’a don gyara ruhaniya na tsarin ikilisiya ba?.
Gaskiyar magana, mutanen nan sun so su shammaci jama’ar Hausawa amma tuntuni mu ka tara kaya kan hanya don haka tayarsu ta taka ta yi faci, kuma duk lokacin da su ka isa ga fakanaiza sai mu yi addu’a injin iska ya kakare! An yi walƙiya.
