
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Honorabul Sa’idu Yusuf Miga, wanda ya shafe wa’adi huɗu a Majalisar Wakilai, ya rasa damar samun tikitin koma wa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027, lamarin da haifar da babban sauyi a siyasar Jihar Jigawa.
Yusuf Miga, ɗaya ne daga cikin tsofaffin ‘yan majalisa da suka fi daɗewa a kujerarsa daga Jigawa, ya rasa tikitin jam’iyyar APC bayan shekaru 16 yana wakiltar al’ummarsa a Majalisar Wakilai.
Sakamakon ya nuna wani sabon sauyi a siyasar jihar, inda masu sharhi ke ganin cewa APC na fuskantar sabon yanayi na canjin shugabanci da sabbin fuska kafin babban zaɓen 2027.
Rashin nasarar Miga ya jawo cece-kuce a tsakanin magoya bayan jam’iyyar da al’ummar mazabarsa, musamman ganin irin dogon lokacin da ya yi yana wakilta.
Tun a shekarar 2003 ne Hon Miga ya fara zama mamba a majalisar a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP kana daga bisani ya koma APC yayin haɗakar ‘yan adawa da ta kai ga nasara a zaɓen 2015.
Ya kuma lashe zaɓen kujerar a 2015, 2019 da kuma 2023, wanda ya mayar da shi ɗaya daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar dokokin ƙasa daga Jihar Jigawa.
