EFCC ta miƙa wa gwamnatin Katsina miliyan ₦837 na badaƙala

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa reshen Kano ta miƙa wa gwamnatin jihar Katsina kuɗaɗe da suka kai N837,485,389 da aka ƙwato daga wasu badaƙalolin karkatar da kuɗaɗen gwamnati. Hukumar ta ce an ƙwato kuɗaɗen ne daga bincike daban-daban da ta gudanar.

A cewar EFCC, an ƙwato N547m daga wata badakalar karkatar da kuɗaɗen haraji da suka fito daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar WHO da MSF. Hukumar ta ce ana zargin wasu ma’aikatan hukumar tara haraji ta jihar da jami’an banki da hannu a lamarin. Ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma sun amsa laifi kuma an yanke musu hukunci, yayin da sauran ke ci gaba da fuskantar shari’a a babbar kotun jihar Katsina.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta sake kwato N290m a wani bincike daban da ake zargin wasu tsofaffin jami’an baitul malin jihar Katsina sun karkatar zuwa asusun kamfanoninsu ba tare da gudanar da wani aiki ko kwangila ba.

Daraktan EFCC na shiyyar Kano, ACE1 Friday S. Ebelo, ya ce kuɗaɗen mallakin al’ummar Katsina ne kuma ya kamata a yi amfani da su wajen ci gaban jihar. Shi ma jami’in hukumar tara haraji ta jihar Katsina, Dr. Kabir Abdullahi Yantumaki, ya gode wa EFCC tare da tabbatar da cewa za a mayar da kuɗaɗen cikin asusun gwamnatin jihar domin amfanin jama’a.

By ukarofi