An tabbatar da Abdul’aziz ‘Yar’adua a matsayin ɗan takarar sanatan Katsina ta tsakiya

Spread the love

Daga UMAR GARBAa Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya jagoranci taron tabbatar da Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Kanal Abdulaziz Musa Yar’adua mai ritaya, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

An gudanar da taron ne a Filin Wasa na Katsina Township Stadium, tare da halartar shugabanni, ‘yan jam’iyya da magoya baya daga sassan yankin.

Shugaban Kwamitin zaɓe na APC daga hedikwatar jam’iyyar, Dakta Yakubu Macciɗo Ahmed, ya ce an cimma matsayar ne bayan yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki da sauran masu neman takarar.

Shi ma shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Yusuf Barmo, ya bayyana cewa sauran masu neman takarar sun janye domin mara wa Sanata Yar’adua baya, domin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal Joɓe, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina Abdulqadir Mamman Nasir, da sauran shugabannin APC.

By ukarofi