Majalisar Tarayya: Masu ruwa da tsaki a Giwa da Birnin Gwari sun buƙaci a mara wa Chiroma baya karo na biyu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari sun yi kira ga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da ta sake bai wa ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Giwa/Birnin Gwari, Hon. Bashir Zubairu, wanda aka fi sani da Chiroman Birnin Gwari, damar tsayawa takara a karo na biyu domin ci gaba da ayyukan ci gaba da ya fara a yankin.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar Giwa/Birnin Gwari Democratic Equity Forum ta shirya ranar Lahadi a Yakawada, inda suka bayyana cewa lokaci ya yi da za a daina siyasar karɓa-karɓa da ta daɗe tana tafiya a yankin, domin a cewarsu hakan na hana samun ci gaba mai ɗorewa da kuma gina shugabanci nagari.
A yayin taron, mahalarta sun bayyana cewa mazaɓar Giwa/Birnin Gwari ta daɗe tana fama da rashin daidaito a fannin ci gaba sakamakon sauya wakilai ba tare da an bai wa waɗanda suka fara ayyuka damar kammala su ba.
Sun ce tsarin karɓa-karɓa da aka daɗe ana yi ya fi karkata ga siyasa maimakon amfani da jama’a, inda suka jaddada cewa ya kamata a dinga bai wa shugabanni dama bisa nagarta, aiki da kuma tasirin da suka yi wa al’umma.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Dauda Yusuf, ya bayyana cewa Chiroman Birnin Gwari ya kawo sauye-sauye masu ma’ana a mazaɓar tun bayan hawansa kujerar ɗan majalisar tarayya.
A cewarsa, yankin ya fara cin moriyar dimokuraɗiyya ta zahiri ta hanyar ayyukan raya ƙasa, tallafa wa matasa da mata, da kuma samar da abubuwan more rayuwa da suka daɗe suna mafarkin samu.
“Mun ga yadda Hon. Bashir Zubairu ya sauya salon wakilci a Giwa da Birnin Gwari. Ya fito da siyasa daga buƙatar kai zuwa amfani na jama’a. Wannan ne ya sa muka ga dacewar mu fito mu bayyana matsayar mu a fili,” iji shi.
Dauda Yusuf ya ƙara da cewa daga cikin ayyukan da Chiroman Birnin Gwari ya aiwatar akwai samar da guraben karatu ga ɗalibai masu tasowa a jami’o’i da manyan makarantu, biyan kuɗaɗen makaranta ga marasa ƙarfi, rabon kayan karatu, da tallafa wa makarantu da kayan aiki.
Ya ce ɗan majalisar ya kuma samar wa matasa dubban guraben ayyukan yi ta hanyar horaswa kan sana’o’i daban-daban da suka haɗa da walda, ɗinki, aikin noma na zamani, kiwon kaji da harkokin kasuwanci.
A cewarsa, baya ga horaswar, an bai wa waɗanda suka ci gajiyar shirin jari domin fara sana’o’insu, lamarin da ya taimaka wajen rage zaman banza da matsalar rashin aikin yi a yankin.
“Matasa da dama a yau sun dogara da kansu saboda tallafin Chiroma. Wasu sun buɗe shaguna, wasu suna sana’o’insu cikin kwanciyar hankali, yayin da wasu ma suka zama masu ɗaukar ma’aikata,” ya bayyana.
Ƙungiyar ta kuma yabawa ɗan majalisar kan ayyukan more rayuwa da ya gudanar, waɗanda suka haɗa da gina da gyaran makarantu, samar da rijiyoyin burtsatse a ƙauyuka da dama, gyaran hanyoyi, samar da fitilun hasken rana a wasu yankuna, da kuma tallafa wa cibiyoyin lafiya da kayan aiki da magunguna.
Haka kuma sun bayyana yadda ya riƙa kai tallafin abinci da kayan masarufi ga marasa galihu musamman a lokutan azumi da bukukuwan Sallah, tare da taimaka wa waɗanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a Birnin Gwari da kewaye.
Dauda Yusuf ya ce dukkanin waɗanda ake hasashen za su nemi kujerar a halin yanzu babu wanda yake da irin ƙwarewa, kusanci da jama’a, da kuma nagartar da Chiroman Birnin Gwari yake da ita.
“Mu a matsayinmu na masu ruwa da tsaki muna kallon abin da zai amfani al’umma ne. A yanzu babu wanda ya kai Bashir Zubairu fahimtar matsalolin wannan mazaɓa da yadda ake magance su. Ya nuna jajircewa, gaskiya da riƙon amana,” inji shi.
Ya ce yankin Giwa da Birnin Gwari na fuskantar manyan ƙalubale musamman matsalar tsaro, talauci da rashin ayyukan yi, don haka akwai buƙatar a ci gaba da bai wa mutum mai hangen nesa dama domin ci gaba da gina tubalin ci gaba.
Wani daga cikin mahalarta taron, Malam Nasiru Isah daga Birnin Gwari, ya bayyana cewa Chiroman Birnin Gwari ya kasance mai sauƙin kai kuma mai sauraron jama’a, saɓanin wasu ‘yan siyasa da ke mantawa da al’umma bayan sun samu mulki.
Ya ce a duk lokacin da aka gabatar masa da matsala, yana ƙoƙarin nemo mafita cikin gaggawa, lamarin da ya sa jama’a da dama suka amince da salon shugabancinsa.
Shi ma Lawal Musa daga Giwa ya ce idan har jam’iyyar ADC tana son ta ƙarfafa matsayinta a yankin, ya zama wajibi ta bai wa Chiroma tikitin takara.
A cewarsa, “idan aka sauya shi da wani a yanzu, za a katse ayyukan alherin da ya fara, kuma hakan zai iya jefa yankin cikin koma baya.”
Masu ruwa da tsakin sun kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar ADC na jiha da na ƙasa da su saurari muradin jama’a maimakon bin matsin lambar wasu ‘yan siyasa masu yi don amfani da kansu.
Sun ce siyasa ya kamata ta kasance hanyar kawo ci gaba, ba hanyar cika yarjejeniyar da ba ta da amfani ga al’umma ba.
A ƙarshe, ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Hon. Bashir Zubairu, tana mai cewa al’ummar Giwa da Birnin Gwari sun riga sun yanke shawarar ci gaba da mara masa baya domin ya kammala ayyukan alherin da ya fara a yankin.

By ukarofi