Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyar APC a jihar Katsina ta amince wa kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina ya zama ɗan takarar kujerar majalisar dattijai a shiyar Daura.
Haka ya biyo bayan zaɓen fidda ɗan takara na cikin gida a jam’iyar da ya gudana a garin Daura tsakanin kakakin majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya Daura da abokin hamayyar sa Alhaji Ahmed Kabir.
Shugaban kwamitin zaɓe da Uwar jam’iya ta ƙasa Dr Yakubu Maccido ya fadi sakamakon zaɓen a tsakanin ‘yan takarar biyu inda ya ce kakakin majalisar ya sami ƙuria 87,000 sai Ahmed Kabir ya sami ƙuria 2000 akan haka Nasiru Yahaya da ya sami ƙuri’u mai rinjaye ya ci zaɓen a matsayin ɗan takarar jam’iyar APC a zaɓen 2027.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da Rt Hon Nasiru Yahaya Daura a matsayin ɗan takarar majalisar dattijai a ƙarkashin jam’iyar APC a shiyar Daura na jihar Katsina.
A jawabin sa kakakin majalisar dokoki ya nuna godiyar sa ga gwamna Dikko Raɗɗa da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC da damar da aka bashi na wannan takara a zaɓen 2027.
Haka Kuma yayi godiya ga ya’yan jam’iyar a ƙananan hukumomi 12 na shiyar Daura da suka zaɓe shi ya zama ɗan takara a majalisar dattijai ta ƙasa.
Sanata Muntari Dandutse da Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua na shiyar Funtua da Katsina sun sami tikitin takarar kujerar su a karo na biyu bayan da abokan takarar su suka janye takarar.
